Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hankali ya Koma Kan Kasashen Afrika 10 Masu Fama da Zazzabin Cizon Sauro


Sauro da yake kawo ciwon zazzabi
Sauro da yake kawo ciwon zazzabi

Nasarar da ake samu akan yaki da zazzabin cizon sauro ya bar hatsarin kamuwa da cutar mafi yawa ga kasashen Afrika 10, in ji wani bincike da Lancet Medical Journal ta buga.

Nasarar da ake samu akan yaki da zazzabin cizon sauro ya bar hatsarin kamuwa da cutar mafi yawa ga kasashen Afrika 10, in ji wani bincike da Lancet Medical Journal ta buga. Nigeriya, Jamhuriyar Congo, Uganda, Ivory Coast, Mozambik, Burkina Faso, Ghata, Mali, Guinea da Togo sun eke dauke da kasha 87 daga cikin 100 na yankunan da suka fi yawan zazzabin ciwon sauro, in ji mujallar.

Binciken ya duba nasasrar yaki da zazzabin cizon sauro, wanda ya sami karin kaimi daga shirin yaki da cutar cizon sauro na shekara ta 2000.

Tun daga wannan lokacin, taimakon kudi ya karu daga dala miliyan 100 (daidai da kudin Uros miliyan 73) a kowacce shekara, zuwa kimanin dala biliyan 2 (kimanin Ero biliyan 1.46).

Masu binciken sun zana hoton yanda fuskar zazzabin cizon sauro ke canzawa wanda aka dauko daga dubban bincike binciken da aka yi a cikin kananan yara daga kasashe 44.

Sun zana hatsari kala uku: “maiyawa”, wanda yake nufin wurare in da fiye da kashi 50 cikin 100 na yawan mutane zasu iya kamuwa da kwayar cutar; matsakaici: (kashi 10 zuwa 50 cikin 100 na yawan mutanen da zasu kamuwa); da kadan: (kasa da kashi 10 cikin dari).

Daga shekara ta 2000 zuwa 2010, yawan mutanen da suke rayuwa a wurin da yake da babban hatsarin kamuwa sun ragu daga miliyan 219 zuwa miliyan 184, raguwar kashi 16 a cikin dari.

Amma mutanen da suke rayuwa a wurin da ke da matsakaicin hatsari sun karu daga miliyan 179 zuwa miliyan 280, karuwar kashi 57 daga cikin dari. Labari mai dadin shine yawan mutanen dake zama a yankuna masu karamin hatsari ya karu daga miliyan 131 zuwa miliyan 219.

Kasashe hudu— Cape Verde, Eritrea, Afrika ta kudu da Ethiopia — sun shiga sahun su Swaziland, Djibouti da Mayotte a kungiyar kasashen da matsayin yaduwar ya ragu sosai, wanda yasa tabbacin kawas da wani buri ne da za’a iya cimma.

Masu binciken sun ce bayanan a yamutse suke, kuma karuwar yawan mutane ya rage kaifin wadansu nasarorin – a cikin wannan karnin, an sami karin kimanin mutane miliyan 200 da aka haifa a wuraren da ake samun zazzabin cizon sauro.

“Da ga shekara ta 2000 zuwa ta 2010, an sami ragowar yaduwar zazzabin cizon sauro a kasashen da ke dauke da cutas,” inji wannan mujallar.

“Duk da haka, a cikin shekara ta 2010, kashi 57 daga cikin 100 na yawan mutane sun cigaba da rayuwa a sassa inda yaduwar ta zama da tsanani, kuma ci gaba da samun taimako daga kowane sashe na duniya ya zama da muhimmanci domin ci gaba da rage karuwar yaduwar ta cutar.”

A Disamba 2da ya wuce, cikin rahoton ta na 2013 kan zazzabin cizon sauro, kungiyar lafiya ta duniya tace daga shekara ta 2000, cece rayuka miliyan 3.3 a dukan duniya.
Duk da haka, cutar cizon sauro ta kashe mutane 627,000 shekarar da ta wuce, yawanci yara a kasashen Afrika da kudancin Asiya.

Wannan kungiyar ta nuna akwai karancin kudi da kuma raguwar maganin rage cutar na artemisinin da kuma sauran kayan rage yaduwar cutar kamar su gidan sauro mai magani suna zama babbar damuwa, in ji su.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG