Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Hukumomin Faransa Basu Kama Madugun Hare-haren Ranar Jauma'a Ba


Mhamed Abdeslam da hukumomin Faransa ke nema ruwa a jallo
Mhamed Abdeslam da hukumomin Faransa ke nema ruwa a jallo

A Faransa mai gabatar da kara a birnin Paris ya fada jiya Laraba cewa, babu tabbas ko an kashe "madugun" kisan hare haren ta'addanci da aka kai kan birnin Paris makon jiya, bayan da 'yansanda suka kai samame a wani ginin gidaje cikin daren jiya a wani kauye da bashi da nisa daga babban birnin kasar.

'Yansand a sun kutsa cikin ginin ne dake kauyen da ake kira Saint-Denis suka kama mutane takwas, amma wanda ake je nema Abdelhamid Abaaoud mai shekarun haifuwa 27, dan Belgium wanda asalinsa dan kasar Morocco ne, baya cikinsu. Dama can anji Abdelhamid yana cika baki cikin watanni da suka wuce cewa, hukumomi sun kasa samunsa.

Hukumomin leken asiri a Turai suna farautarsa na tsawon watanni, amma sun kasa kama shi,yana yiwa hukumomi ba'a cewa yana balaguronsa gaba gadi tsakanin Turai d a Syria ba tareda an ganeshi ba.

Ahalinda ake ciki kuma, samamen da jami'an tsaron Faransa suka kai da asubahin jiya Laraba yayi nasarar tarwatsa wani gungun 'yan ta'adda.

XS
SM
MD
LG