Tun bayan da aka yankewa matar tsohon shugaban kasar Ivory coast hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru mutane daga bagarori daban-daban na ci gaba da tsokaci kan wannan hukunci.
A ranar Talatar da ta gabatab wata kotu ta samu Simone Gbagbo da laifin tunzura rikicin da ya biyo bayan zaben shekarar 2010, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 3,000.
Sai dai wasu masu sharhi na cewa duk da hukuncin ya yi dai dai zai iya farfado da kiyayya tsakanin magoya bayan tsohon Shugaba Laurent Gbagbo da magoya bayan Alassane Ouattara.
“Lallai wannan hukunci ya hada hayaniya tsakanin tsohon shugaba Gbagbo da sabon shugaba, saboda sun gwada cewa hukuncin ya yi tsauri ya yi yawa” In ji Usman Jah Ustaz, wani dan jarida a Ivory Coast.
Sai dai mai sharhin ya ce hukuncin zai iya zama darasi ga sauran matan shugabannin kasar domin wannan shi ne karo na farko da aka taba yanke wannan hukunci a wata da ta taba irin wannan mukami.