Jumma’a, Maris 27, 2015 Karfe 20:07

Najeriya

Ibrahim Babangida Da Olusegun Obasanjo Sun Gana Kan Tsaro A Najeriya

Tsoffin shugabannin biyu sun zauna suka yi shawara kan hanyoyin da suka fi dacewa na kawo karshen tashe-tashen hankula da zub da jini a kasar

Tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida
Tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida

Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, da tsohon shugaba Olusegun Obasanjo, sun gana na tsawon lokaci domin tattauna matsalolin tsaro da suka dabaibaye Najeriya a daidai wannan lokacin.

Da yake tabbatar da wannan ganawa ta su ga masu neman labarai, Janar Babangida ya ce ya kamata kowane dan Najeriya ya sanya hannu a kokarin kawo karshen wannan ukuba da ta far ma kasar.

A wata hirar da yayi da wakilin Muryar Amurka, Mustapha Nasiru Batsari, janar Babangida ya ce zasu ci gaba da wannan kokari nasu, kuma ko da ta kama ne ma, zasu sake sanya rigunansu na soja domin tabbatar da ci gaba da dorewar Najeriya a zaman kasa daya.

Ga bayanin Janar Babangida a wannan hira ta su...

Batun Tsaro A Najeriya

Hira Da Janar Ibrahim Badamasi Babangida

An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: Linus Kazzah Daga: Gumel - Kachia Kad. state
14.08.2012 15:39
zaman lafiya a kasata nigeria sai da adalci, don haka tsoffofin shugabannai su sa ido akan aikata gaskiya da adalci, wannan shine mafita.


by: Babayola umar Daga: Adamawa a Nijeriya
13.08.2012 13:25
A gaskiya ya kamata dattaban arewa a najeriya sutashi, saboda goodluck yanaso yaga bayan arewa da jama'anta baki daya.


by: Abdulhamid Almustapah
31.07.2012 05:20
Allah yasa hakane yafi zama alkhairi garemu bakidaya,Amma dai wallahi kugayawa agola ya tabbata bazashiyi gado ba.

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti