Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Na Cigaba da Tattaunawa Akan Shirin Nukiliya


Shugaban Iran Hassan Rouhani
Shugaban Iran Hassan Rouhani

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce kasarsa tana cigaba da tattaunawa da manyan kasashen nan shida akan shirin nukiliyar kasar.

Shugaba Hassan Rouhani na Iran yace yanzu haka kasar tana tattaunawa da manyan kasashen nan 6 game da kai karshen tattaunawar da suke yi game da sarrafa makamin Nuclear amma ba da yan majilisar dokokin kasar Amurka ba.

Shugaba Rouhani yayi wannan furucinne jiya sailin da yake tsokaci akan bayanan abinda ke faruwa anan Washington ranar talata inda shugaba Obama yace zai sawa dokar hannu amma kuma kasancewar ta doka zai diogara ne idan yan majilisar sun sake duba wannan batu.

A lokacin da yake wa dubun dubatan yan kasar na Iran jawabi a arewacin birnin Rasht shugaba Rouhani ya tabbatar musu cewa kafin yasa wa wata yarjejeniya hannu sai an soke daukacin takunkunmin da aka sawa kasar sa.

Kwamitin kula da harkokin hulda da kasashen waje na majilisar dattijan na Amurka yace akwai bukatar duba wannan yarjejeniyar har na tsawon kwanaki 30.

Haka kuma sun bukaci shugaba Obama da bayan ko wasu kwanaki 90 ya tabbatar ko kasar ta Iran tana bin wannan yarjejeniyar sau da kafa, inda duk ta saba to a mayar da wannan takunkumin.

Jiya ne dai sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yace yana da kwarin gwiwar cewa za a cimma matsaya na karshe da kasar ta Iran game da wannan batu na Nuclear

XS
SM
MD
LG