Jumma’a, Nuwamba 27, 2015 Karfe 05:32

Labarai / Sauran Duniya

Iraqi Ta Soke Yarjejeniyar Sayan Makamai Data Kulla Da Rasha.

 Frayin ministan Rasha Dmitry Medvedev yake gaisawa da PM Nouri Al-Maliki,na Iraqi. Frayin ministan Rasha Dmitry Medvedev yake gaisawa da PM Nouri Al-Maliki,na Iraqi.
x
 Frayin ministan Rasha Dmitry Medvedev yake gaisawa da PM Nouri Al-Maliki,na Iraqi.
Frayin ministan Rasha Dmitry Medvedev yake gaisawa da PM Nouri Al-Maliki,na Iraqi.
Tana kasa tana dabo kan  yarjejeniyar cinikin makamai tsakanin Rasha da Iraqi na zunzurutun kudi dala milyan dubu hudu da metan.

Kakakin PM Iraqi Nouri al-Maliki, ya fada jiya Asabar cewa an soke cinikin, sabo da gwamnatin kasar tana shakkar an saka rashin gaskiya cikin yarjejeniyar. Amma wasu jami’an kasar suka ce ana dai sake nazarin shirin baki dayansa.

A cikin watan jiya ne Bagadaza da Moscow suka sanya hanu kan yarjejeniyar.
Rahotanni sun ce da za a sa jiragen yaki masu saukar angulu samfirin Mi-28 guda 30 cikin yarjejeniyar cinikin, idan har hakan ya kasance, Rasha zata zama ta biyu wajen samarwa Iraqi kayan yaki, bayan Amurka.

Kamfanin dillancin makamai na Rasha yaki yace uffan kan wannan batu. Sai dai babu karin bayani ko Iraqi tana auna zargin cin hanci da  rashawa kan Moscow ne ko kuma akan jami’an gwamnatin kasarta.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Sauti

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye