Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ISIS Ta Ce Ita Ce Ta Kai Hari Ta KAshe Masu Gadin Shugaban Kasar Tunisiya


Kungiyar ISI ta dauki alhakin harin bam da aka kai talata cikin wata motar bas dake dauke da zaratan sojoji masu gadin shugaban kasar, inda aka kashe mutane akalla 12.

Cikin wata sanarwar da aka buga yau laraba a shafukan sada zumunci na intanet, kungiyar ta 'yan ta'adda ta ce wani tsagera mai suna Abu Abdullah al-Tunisi, shi ne ya kai harin, inda ya shiga cikin motar da suke tafiya ya tayar da bam ya kashe abinda ta kira "kafirai" su 20.

Wannan bas tana tafiya a tsakiyar Tunis, babban birnin kasar, a lokacin da wannan lamarin ya faru.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Tunisiya, ta fada yau laraba cewa an kai harin ne da nakiya mai nauyin kilo 10 wadda aka boye cikin jakar da ake ratayawa a baya ko kuma a cikin riga ta kunar-bakin-wake. Ma'aikatar ta fada cikin wata sanarwa cewa gawa ta 13 da aka samu a wurin, an yi imanin ta dan ta'addar da ya tayar da wannan bam ne, tana mai fadin cewa ana yin gwajin kimiyya domin gano asalinsa.

Har ila yau, Tunisya ta bada sanarwar rufe bakin iyakarta da Libya ta kasa na tsawon kwanaki 15.

XS
SM
MD
LG