Talata, Satumba 01, 2015 Karfe 21:17

Labarai / Sauran Duniya

Isra'ila Da Hamas Suna Ci Gaba Da Musayar Wuta Da Rokoki

Wata garkuwar cafke rokoki Isra'ila ta harba daga yankinta dominn tare rokoki daga yankin Gaza.Wata garkuwar cafke rokoki Isra'ila ta harba daga yankinta dominn tare rokoki daga yankin Gaza.
x
Wata garkuwar cafke rokoki Isra'ila ta harba daga yankinta dominn tare rokoki daga yankin Gaza.
Wata garkuwar cafke rokoki Isra'ila ta harba daga yankinta dominn tare rokoki daga yankin Gaza.
Isra’ila da mayakan sa kai na Hamas sun yi musayar wuta da  rokoki, har  daya rokar daga yankin Falasdinu ta dira a wani fili a wajen birnin kudus, a jiya jumma’a.
Jana'izar wani kwamandan Hamas da Isra'ila ta kashe.Jana'izar wani kwamandan Hamas da Isra'ila ta kashe.
x
Jana'izar wani kwamandan Hamas da Isra'ila ta kashe.
Jana'izar wani kwamandan Hamas da Isra'ila ta kashe.

Nan da  nan jiniyoyi suka cika binrin  na kudus, amma jami’an Isra’ila suka ce babu wanda ya jikkata ko barna ga dukiya. Kungiyar Hamas ta dauki alhakin kai harin.

Isra’ila ta maida martani ta wajen  bada umarni ga sojojinta na wucin gadi suyi damara watakil wannan mataki na kai farmakin soja daga kasa zuwa zirin na Gaza. Haka kuma ta rufe manyan hanyoyi dake kusa  da Gaza.

Akwai fargabar lamarin da yake wanzu tsakanin Isra’ila da  Hamas zai kai ga barkewar yaki gadan gdana. PM Masar Hashem Kandil ya kai ziyara Gaza, ind a yayi aalkwawarin Masar zata sadaukar da kai da yin kokari tukuru wajen ganin an tsagaiata wuta. Amma a Alkahira shugaban kassar Mohammed Morsi yayi Allah wadai d a abinda ya kira takalar Istra’ila.

Duk da zazzafar lafazin Mr. Morsi, shugaban Amurka Barack Obama ya kira shugaban na Masar ta wiyar tarho jiya jumma’an, domin su tattauna kan rikicin, daga nan kuma yay a yabawa Masar kan kokari da take yin a warware zaman dar dar tsakanin Isra’ila da Hamas.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti