Hukumomin Isra’ila sun ce sun sassafto da takunkumi da hana shiga da fidda kayan da aka azawa yankin Zirin Gaza, domin a sami sukunin shigar da kayan gine-gine domin amfanin masu son gina gidaje a yankin na Falasdinawa.
Hakan ya bada damar shigar da mafi yawan kayan gine-ginen da aka sayosu ne daga kasar Misra kan kudin da aka kiyasta yawansu ya kai Dala Miliyan $400 domin ginin gidajen maras galihun da kasar Qatar ke shirin yi a Zirin Gaza.
A shekarar 2007 ce Isra’ila ta kakabawa yankin falasdinawan takunkumin hana shigar da kaya bayan da mayakan Hamaz suka kwaci ragamar mulkin gudanar da yankin.