Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iyayen Cibok na Shirin Zanga-zanga


Iyayen dalibai mata wadanda aka sace a makarantar Sakandare dake Cibok.
Iyayen dalibai mata wadanda aka sace a makarantar Sakandare dake Cibok.

​Iyayen yaran nan mata dalibai da aka sace a makarantar Sakandare dake Cibok sun fara kosawa da yadda neman yaran yake gudana, shiyasa ma suke tanadin yin zanga-zanga.

Tun bayan sace yaran, 39 daga cikinsu sun kubuto inda yanzu 234 ke rike a hannun ‘yan bindiga wadanda ake zaton ‘yan Boko Haram ne.

Hukumar tsaron Najeriya a baya ta fitar da sanarwar ceto kusan duka ‘yan matan, kuma daga baya ta janye kalaman nata.

Shi kuwa gwamnan jihar Borno Kashim Shettima yayi alkawarin bada naira miliyan 50 ga duk wanda ya taimaka aka ceto matan.

Ya zuwa yanzu dai hukumomi basu fitar da wani bayani ba game da inda aka kwana, a yunkurin ceto yaran wadanda yawancinsu matasa ne.

Daya daga cikin iyayen ya nuna damuwarshi matuka akan yadda hukumomi suka gaza wajen sanar dasu inda aka kwana.

“Batun yarannan an barmu a cikin duhu, babu abunda akayi. Ba’a yi mana komai ba”, a cewar daya daga iyayen.

Mutumin ya kara da cewa “yanzu abinda iyaye suke shirin yi “demonstrations” ne”.

Ya zuwa yanzu dai ba’a bayyana lokacin da za’a yi wannan zanga-zanga ba, amma an shirya za’a yi shine a karamar hukumar ta Cibok dake jihar Borno.

Yanzu haka sama da makonni biyu kennan da sace yara mata dalibai su sama da 200 daga makarantar Sakandarin Gwamnati dake Cibok a jihar Borno, a lokacin da suke rubuta jarrabawar karshe ta fita daga makaranta.
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:38 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG