Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jagoran Juyin Mulkin Kasar Burkina Faso Ya Gurfana Gaban Kotu


Janar Gilbert Diendere (a tsakiya) wanda ya yi juyin mulkin da bai dore ba
Janar Gilbert Diendere (a tsakiya) wanda ya yi juyin mulkin da bai dore ba

An gurfanar da Janar Gilbert Diendere, hafsan sojan nan da ya jagoranci juyin mulki a Burkina Faso da bai sami nasara ba cikin watan jiya, tareda wani babban jami'in gwamnati, kan zargin ya bada goyon bayan a hambare gwanatin kasar ta Burkina Faso.

Jiya Talata aka gurnafar da Janar Gilbert Diendere tareda Djibrilla Bassole, tsohon ministan harkokin waje, wadanda suke fuskantar zargin kai hari kan "madafun tsaron kasar".

A lokacin da suka ayyana juyin mulkin, dogarawan fadar shugaban kasa wadanda suke karkashinJanar Diendere, sun tsare shugaban kasar na wucin gadi da Firayim ministan, da wasu minisitoci. Sunyi haka ne domin su nuna rashin jin dadinsu kan matakin hana magoya bayan tsohon shugaban kasa Blaise Compaore shiga takara a zaben kasar da ake shirin yi.

Janar Diendere ya rike iko na kusan mako daya, amma matsin lamba daga sojojin kasar, da masu zanga zanga da kuma kungiyar raya tattalin arzikin kasashe dake yammacin Afirka suka tilasta masa yayi murabus.

A makon jiya ne Janar Diendere yayi saranda bayan da yayi shawarwari da jami'an kasar a Ouagadougou.

Djibrilla Bassole, wanda ya rike mukamin ministan harkokin waje zamanin mulkin shugaba Compaore, ya musanta ya na da hanu a juyin mulkin.

Ana ci gaba da tsare mutanen biyu.

XS
SM
MD
LG