Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jakadiyar Amurka a MDD Zata je Kasashen Afirka Masu Fama da Cutar Ebola


Jakadiyar Amurka a MDD Samantha Power.
Jakadiyar Amurka a MDD Samantha Power.

Jakadiya Samantha Power za ta kai ziyara kasashen Guinea da Laberiya da kuam Saliyo.

Jakadiyar Amurka a MDD Samantha Power za ta ziyarci wuraren da su ka zama matattarar barkewar cutar Ebola domin ta yiwa sauran kasashen duniya kaimin kara kokarin yakar cutar.

Samantha Power za ta ziyarci kasar Guinea da Laberiya da kuma Saliyo. Ta shaidawa manema labarai a jiya Asabar cewa zuwa da kan ta ta ganewa idanun ta halin da ake ciki a kasashen ya fi.

Samantha Power za ta ziyarci cibiyoyin tsara dabarun yaki da Ebola, kuma ta gana da jami'an gwamnatocin kasashen, sannan ta hadu da kwararrun likitocin Amurka da kuma sojojin kasar masu yaki da cutar.

Kasashen Guinea da Laberiya da Saliyo su na cikin dabaibaiyin matsalar cutar Ebola wadda ta hallaka mutane fiye da dubu 5 daga cikin wadanda aka tabbatar sun kamu da ita su fiye da dubu 10. Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ce a gaskiya yawan na iya fin haka saboda iyalai da dama sun yi kokarin yin inyar masu fama da cutar a gidajen su.

Haka kuma a jiya Asabar MDD ta tura kayan agajin gaggawa mai nauyin ton daya wato kilogra dubu daya zuwa kasar Mali bayan ta bada labarin mutuwar mutum na farko a kasar sanadiyar cutar Ebola.

Wata yarinya 'yar shekaru biyu da haihuwa ce ta mutu ran Jumma'a a kasar ta Mali bayan fitowar su daga kasar Guinea.

Sansanin killace wadanda suka yi jinyar Fanta Kone 'yar shekara biyun da ta mutu ran Jumma'a a Mali sanadiyar cutar Ebola
Sansanin killace wadanda suka yi jinyar Fanta Kone 'yar shekara biyun da ta mutu ran Jumma'a a Mali sanadiyar cutar Ebola

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce ta bas yarinyar da iyayen ta suka je Mali, saboda haka watakila cutar ta harbi wasu mutane a kasar ta Mali.

A halin da ake ciki kuma, gwamnan jahar Illinois Pat Quinn ya bada umarnin daukan matakin sanya duk wanda ya je jahar daga Guinea ko Laberiya ko Saliyo, cikin zaman kullen dole na kwanaki 21a killace. Umarnin ya shafi duk wanda yayi mu'amala kai tsaye da mai cutar Ebola.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG