Jumma’a, Fabrairu 27, 2015 Karfe 00:19

Kiwon Lafiya

Jihar Neja ta Baiwa Yara Rigakafin Polio

Darektan hukumar kiwon lafiya matakin farko na Jihar Neja, Dr. Yabagi Aliyu, yace ya zuwa yanzu, alkaluma sun nuna yara fiye da miliyan biyu da rabi suka karbi wannan magani a zagaye na uku na rigakafi a wannan shekara.

Garba Suleiman
Yara ‘yan kasa da shekara biyar su fiye da miliyan biyu da rabi ne aka diga musu ruwan maganin rigakafin cutar shan innam ko Polio, a Jihar Neja, a zagaye na uku na aikin rigakafi a wannan shekara.
 
Darektan hukumar kiwon lafiya matakin farko na Jihar Neja, Dr. Yabagi Aliyu, yace har yanzu sun a ci gaba da tattara alkaluma, amma dai ya zuwa yanzu, sun samu fiye da wannan adadin.
 
Darektan yace har yanzu sun a samun matsalolin wasu iyayen dake hana yaransu karbar wannan magani, koda yake kalilan ne. Yace da yawa daga cikinsu, sun sauya tunani a bayan da aka yi musu bayani na wannan maganin rigakafin da kuma muhimmancinsa.
 
Ya bayyana wannan zagaye na rigakafin cutar Polio da cewa an samu nasararsa sosai.
 
Abu mafi muhimmanci da hukumomi suka dukufa ga yi shi ne tabbatarwa da jama’a sahihancin wannan maganin, a bayan jita-jitar da aka yi ta yadawa kan cewa yana hana haihuwa.
 
Wani babban jami’in ma’aikatar kiwon lafiya ta tarayya, Dangana Sa’adu, yace a matsayinsa na Musulmi kuma jami’in kiwon lafiya zai iya rantsuwa kan sahihancin wannan magani, yana mai yin watsi da zargi maras tushe da wasu keyi kan cewa wannan magani yana hana haihuwa.
 
Yace an kai wannan magani an gwada shi a dukkan manyan kasashen Musulmi na duniya, kamar Saudi Arabiya, Indonesiya, Malaysia da sauransu, kuma ba a taba samun wani abu maras kyau ko mai illa a cikinsa ba.
 
Sama Da Yara Miliyan 2.5 Aka Yi Ma Rigakafin Polio A Jihar Neja - 2'24"
Sama Da Yara Miliyan 2.5 Aka Yi Ma Rigakafin Polio A Jihar Neja - 2'24"i
|| 0:00:00
...    
🔇
X
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti