Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Yakin Amurka Da Ba Su Da Matuka Sun Kai Farmaki A Pakistan.


Samfurin jiragen yakin Amurka da ba su da matuka.
Samfurin jiragen yakin Amurka da ba su da matuka.
Jami’ai a Pakistan sunce wani hari daga jirgin sama mara matuki ya kashe mutane 8 da ake zargi mayakan sa kai ne, a kusa da iyakar kasar da Afghanistan, yankin da ake zato na karkashin ikon Taliban.

Jami’ai sunce ana kyautata zaton akwai wani kusan al-Qaida a cikin wadanda harin ya kashe a kusa garin Mir Ali, a arewacin Waziristan.

Harin da aka kai a safiyar talata na daya daga cikin hare-hare na baya-bayan nan da aka kai a fadin wannan yanki. Ranar lahadi da ta gabata, jami’an Pakistan sunce wasu mutane guda 9 da ake zaton mayakan Taliban ne suka halaka daga harin da jiragen yaki da basu da matuka a ciki, a wata mafakarsu, a kudancin Wziristan.

Gwamnatin Pakistan ta fito fili tayi Allah wadai da harin da wadannan jirage suke kaiwa a matsayin keta diyaucin kasar, amma ana kyautata zaton akwai taimakon ma’aikatar leken asirin Pakistan wajen kai wadannan hare-hare.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG