Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Sama Mai Anfani da Zafin Rana Yana Kan Tafiyar Cika Kilomita Dubu 35


Jirgin sama mai anfani da zafin rana
Jirgin sama mai anfani da zafin rana

Jirgin nan mai amfani da zafin rana ya ci gaba da tafiya a yunkurin da yake yi na tafiyar kilomita dubu 35, na gewaye duniya ba tareda amfani da koda digon mai ba.

Jirgin da wani dan kasar Siwtzerland yake tukashi ya tashi daga tsakiyar Japan a safiyar yau Litinin bayan jinkirin wata guda da ya sauka babu shiri a can.

Jirgin da ake kira Solar Impulse da turanci karkashin matuki Andre Borshberg, wanda shi daya ne daga cikin wadanda suka kera jirgin, ya tashi ne yau daga wurin da ake kira Nagoya a kasar ta Japan a yunkurin bi takan tekun Pacific zango mafi tsawo a balaguron da jirgin zai yi.

Masu lura da harkokin jirgin suka ce idan yanayi akan tekun na Pacific bashi da kyau za'a fasa tafiyar. Amma za'a iya kaiwa wani nisan da babu halin a koma Japan a kokarin ketare tekun na Pacific.

Masana suka ce akwai hadari a kokarin ketare kan tekun zuwa Hawaii, domin babu wuri da jirgin zai iya sauka idan bukatar haka ta gaggawa ta taso.

Tun farko ba'a shirya jirgin ya sauka a Japan ba, amma aka karkata shi zuwa kasar a farkon wannan wata, kan hanyarsa daga Nanjing dake gabashin kasar China zuwa Hawa'ii saboda munin yanayi.

Jirgin mai lakabin SI an shirya zai ci gaba da tafiyarsa a makon jiya, amma dab da jirgin zai kama hanya aka soke tashinsa saboda munin yanayi.

Jirgin, masana kimiyya biyu 'yan kasar Switzerland Bertrand Piccard da Borschberg ne suka kirkoro shi. Ya dauke kimanin shekaru 12 kafin su kammala aikin kera shi.

XS
SM
MD
LG