Talata, Satumba 16, 2014 Karfe 09:26

Kiwon Lafiya

Kananan hukumomi 200 suna fuskantar barazanar yaduwar cutar polio,

Babban jami’ain kiwon lafiya na jihar Bauchi yace kananan hukumomi maitan daga cikin 774 na Najeriya suna fuskantar cutar polio

Ana ba wani dan yaro maganin cutar shan inna
Ana ba wani dan yaro maganin cutar shan inna
Kahli Abdu

Babban jami’ain kiwon lafiya na jihar Bauchi yace kananan hukumomi maitan daga cikin 774 na Najeriya na cikin hadarin barkewar cutar shan inna.

Sakataren cibiyar Nisser Umar ya bayyana haka ne yayin kaddamar da aikin rigakafin shan inna da kari da aka gudanar a jihar a Karamar hukumar Ganjuwa,

Bisa ga cewarshi, kananan hukumomi 15 daga cikin ishirin na jihar na daga cikin kananan hukumomin dake cikin hadarin barkewar cutar. Sakamakon gaza yiwa kananan yara da dama rigakafi da kuma kaurar da tafiyar al’umma daga jiha zuwa jiha.

Mr. Umar ya yi kira ga iyaye su tabbata an yiwa ya’yansu rigakafi, yayinda ya  bayyana cewa, an kara yawan ma’aikatan da zasu gudanar da aikin rigakafin. Bisa ga cewarshi, gwamnati jiha tare da hadin guiwar kananan hukumomi ta sayi magani da za a iya yiwa yara miliyan daya da dubu dari tara  rigakafi.

Za a dauki kwana hudu ana gudanar da aikin rigakafin.

An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Rediyo/Sauti

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +1-202-619-0548 ko kuma +1-202-619-0551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +1-202-205-9942.
 

Audio Shirin Safe     Rumbun Shiri    Live

           0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi  Rumbun Shiri   Live

           0700 - 0730 UTC 

Audio Shirin Rana     Rumbun Shiri   Live

            1500 - 1530 UTC 

Audio Shirin Dare     Rumbun Shiri   Live

            2030 - 2100 UTC