Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KANO STATE: Zata Gina Layin Dogo tare da Wani Kamfanin China


Layin dogo da jirgin kasa
Layin dogo da jirgin kasa

Gwamntin Kano tare da wani kamfani daga kasar China zata gina layin dogo a Kano da kewaye

Tuni dai gwamnatin ta Kano ta sanya hannu akan wata takardar yarjejeniyar fahimta tsakaninta da kamfanin domin tsara yadda aikin zai kasance.

Gwamnan jihar Dr Abdullahi Ganduje ya fayyace makasudin kaddamar da aikin. Yace jihar ta fi kowace jiha yawan jama'a a Najeriya saboda haka maganar zirga zirgan jama'a magana ce babba da yakamata gwamnati ta duba.

Yace zamani ya nuna yawan motoci da babura ba su ne zasu kawo zirga zirga mai tsafta ko inganci ba musamman batun kiwon lafiya. Motoci masu yawa suna gurbata iska da mutane ke shaka.

Abu mafi mahimmanci shi ne yadda mutane zasu yi zirga zirga cikin sauki. Saboda haka gwamnatin Kano ta ga yakamata ta inganta sufuri domin yana cikin abubuwan da ake gane babban birni ko ya bunkasa ko kuma yana cikin matsala ne.

To saidai layin dogo ya dogara ne akan samun isasshiyar wutar lantarki wadda yanzu Kano ke fama da ita. Amma gwamnan yace maganar wutar lantarki magana ce da shugaban kasa ya baiwa mahimmanci. Yayi alkawarin ingantata kuma daga hawarsa mulki an fara samun canji. Ita ma jihar tana aiki akan samarda wuta saboda bunkasa masana'antu.

Duk da cewa gwamnan bai fadi adadin kudaden da aikin zai lakume ba kuma inda kudin zai fito amma abun da aka sani ne cewa kamfanin ne zai gina layin da kudinsa kana masu anfani dashi su dinga biyan kudin sufuri. Sai kamfanin ya mayarda kudinsa tare da riba kafin ya mika layin ga gwamnati.

Ga rahoton Ibrahim Mahmud Kwari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG