Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Kudi a Sudan Ta Kudu Ya Jefa Miliyoyin Mutane cikin Yunwa


Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kir
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kir

Kidigdigar da Majalisar Dinkin Duniya (MDD) tayi ya nuna cewa miliyoyin mutane a Sudan Ta Kudu karancin kudi ya jefasu cikin cikin wata matsananciyar yunwa

Majalisar Dinkin Duniya tayi gargadin cewa a Sudan ta kudu miliyoyin mutane ne suke fuskantar matsanancin yunwa sabaoda karancin kudi. Lisa Schlein ta aikowa MA wannan rahoto daga Geneva inda wani babban jami’in MDD yace ana bukatar fiyeda dala milyan metan da talatin cikin watanni biyu masu zuwa domin kaucewa fadawa cikin mummunar bala’in rayuwa.

Kimanin ‘yan kasar milyan daya ne aka tilastawa gudu daga gidajensu cikin kwanaki dari da suka wuce.Wasu fiyeda dubu dari takwas an raba su da muhallansu amma suna cikin kasar ta Sudan ta kudu. Sauran suna gudun hijira a kasashe makwabta.
Mai kula da harkokin MDD a Sudna ta Kudu Toby Lanzer, yace wannan rikicin yana iya kara muni a bana idan har dubun dubatan ‘yan Sudan ta kudu suka gudu daga kasar.

Ya lura cewa an yi kaca-kaca da birane masu yawa tun lokacinda rikici ya barke tsakanin sojojin gwamnati da ‘yan hamayya a tsakiyar watan Disemban bara. Yace kasuwannai sun watse, kuma kusan dukkan harkar cinikayya tsakanin kasar da Ethiopia da Uganda da kuma Kenya sun tsaya cik. Yace mutanen kasar sun tasamma tagayyara.

Lanzer yace “Muna da mutane milyan uku da dubu dari bakwai wadanda suke fuskantar kasadar fadawa cikin matsanancin ‘yunwa.Kuma muna cikin watan Afrilu da Mayu lokacinda ake bukukuwan faduwar damuna. Wannan lokacin ne ake fara ruwan sama kuma mutane suke fara aiki a gonakinsu.A lokacinne kuma suke kula da shanunsu, da tumaki da awakinsu. Amma yanzu basa iya yin haka saboda babu tsaro. Ba zasu iya zuwa gonakinsu da walwalar da ake bukata ba."

Lanzer yana gayawa masu bada tallafi na kasa da kasa da kuma jami’an gwamnatoci cewa miliyoyin ‘yan kasar Sudan ta kudu suna bukatar agaji domin su rayu.Haka nan yace akwai buktar a taimaki mutanen domin suma su sami sukunin taimakawa kawunansu.

Yace ana bukatar kudi yanzu domin a tabbatar da cewa mutane suna da abinci domin su sami karfin aiki a gonakinsu.

Ya gayawa Muryar Amurika cewa yana da muhimmancin gaske a baiwa manoma iri da kayan aiki domin su fara shuke shuke yau.

Lanzer ya kara da cewa “Idan har ba a sami damar gudanar da ayyukan gona a daminar ban aba, za’a sami mummunar koma baya kan wadatar abinci, domin abunda zai aukawa kasan nan, zai shafi mutane kimanin milyan bakwai, zai kasance mummunar bala’I rabon da nahiyar Afirka ta ga irinsa tun a wajajen shekarun 1980. Abunda muke kokarin hana aukuwarsa kenan.Kuma, Allah Ya sawwaka, idan har da haka zata faru zai ci rayuka da dukiya mai yawan gaske. Domin haka, akwai bukatar a dauki mataki yanzu ko kuma a kashe kudade masu yawa nan gaba fiyeda abunda da za’a kashe yanzun."

Lanzer yace samar da dala milyan metan da 32 yanzu zai taimakawa hukumomi su adana abinci da kayan masarufi a wuarre da suka dace kamin damina ta fadi sosai, wacce idan ta kankama hanyoyin mota basa biyuwa sam sam.
XS
SM
MD
LG