Alhamis, Agusta 21, 2014 Karfe 17:59

Afirka

Kasar Mauritaniya Ta Mikawa Libya tsohon babban jami'in leken asirin gwamnatin Gaddafi

Tsohon shugaban hukumar leken asiri na Libya zamanin mulkin Gadhafi-el-SanousiTsohon shugaban hukumar leken asiri na Libya zamanin mulkin Gadhafi-el-Sanousi
x
Tsohon shugaban hukumar leken asiri na Libya zamanin mulkin Gadhafi-el-Sanousi
Tsohon shugaban hukumar leken asiri na Libya zamanin mulkin Gadhafi-el-Sanousi
Kamfanin dillancin labarai na Mauritaniya yace kasar ta mikawa Libya tsohon babban jami’uin leken asiri na marigayi shugaba Muammar Gaddafi, Abdullah al-Sanusi, inda ake sa ran zai gurfana a gaban shari’a.

An kama al-Sanusi a watan Maris a bayan da ya saci jiki ya shiga kasar Mauritaniya bayan da ya batar da kamanni ya kuma yi amfani da fasfo na karya. Tun lokacin, hukumomin Libya sun nemi a mika musu tsohon jami’in leken asirin wanda kotun duniya ma take nema.

Mauritaniya ta nace a kan cewa zata gurfanar da shi gaban shari’a a saboda ya shiga kasar ba tare da izni ba. Amma jami’an gwamnati sun tabbatar cewa al-Sanusi ya bar Mauritaniya yau laraba a cikin wani jirgin saman da ya doshi kasar Libya.

A watan Yuni kotun bin bahasin manyan laifuffuka ta duniya ta bayar da takardar iznin kama al-Sanusi tana mai fadin cewa yana da alhaki, a zaman mai masaniya ko wanda ya bayarda umurnin aikata laifuffuka biyu na cin zarafin bil Adama, ciki har da kisan kai da danniyar siyasa.

Rediyo/Sauti

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +1-202-619-0548 ko kuma +1-202-619-0551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +1-202-205-9942.
 

Audio Shirin Safe        MP3

Audio Shirin Rana       MP3

Audio Shirin Dare       MP3

Audio Mu Tattauna       MP3