Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Rwanda ta Bukaci Wadanda Suka Fito daga Amurka da Spain Su Dinga Kiran Jami'an Kiwon Lafiya har na Kwanki 21


Anastase Murekezi, Firayim Ministan Rwanda
Anastase Murekezi, Firayim Ministan Rwanda

Cikin kasashen Amurka da Spain aka samu bullar cutar ebola baicin kasashen Liberiya, Guinea da Saliyo

A dai-dai wannan lokaci da aka wanke Najeriya daga jerin kasashe dake dauke da kwayar cutar Ebola, kasar Rwanda dake gabashin Afirka ta bada umarnin cewa matafiya daga Amurka da Spain su dinga kiran jami’an kiwon lafiyar kasarta kullum suna bada bayanan lafiyarsu.

Wadannan kasashe guda biyu sune kadai kasashen dake wajen nahiyar Afirka, da suka samu bullowar kwayar cutar mai ban tsoro.

Dole ne duk wanda ya taho daga, ko ya ziyarci wadannan kasashen guda biyu ya kira jami’ai kullum har na tsawon kwanaki 21.

A halin yanzu dai Ruwanda bata da wannan cuta, kuma ta dauki damarar hanata shiga kasar.

Bugu da kari Ruwanda ta haramtawa matafiya daga inda annobar ta barke wato Guinea, Laberiya da Saliyo shiga kasarta. Ta ma hana matafiya daga Senegal zuwa, duk da cewa sau daya kacal aka samu bullowar cutar a Senegal.

Hukumar tsaron cikin gida a nan Amurka na bukatar duk matafiya daga Laberiya, Guinea da Saliyo ya shigo nan Amurka ta daya daga cikin tashoshin jiragen sama 5 da ake gudanar da binciken Ebola mai tsanani.

Wadannan tashoshin jiragen sama suna biranen Atlanta, Chicago, New York, Washington, da Newark da ma New Jersey.

Dama mafi yawancin lokuta kaso 94 cikin dari na matafiya masu zuwa nan Amurka daga wadannan kasashe guda uku, ta wadannan tashoshi suke shigowa.

A halin da ake ciki kuma, a birnin Dallas, ma’aikaciyar kiwon lafiyar nan wadda ta dauki kwayar cutar daga dan Laberiyan nan, ta fara samun birnin Washington. sauki. Ana yi mata jinya a wani asibiti dake kusa da nan

XS
SM
MD
LG