Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Larabawa Zasu Dauki Mataki Akan 'Yan Tawayen Houthi


Mayakan sa kai na 'yan tawayen Houthi a kasar Yemen
Mayakan sa kai na 'yan tawayen Houthi a kasar Yemen

Kashen Larabawa sun lashi takobin daukan mataki akan 'yan tawayen Houthi idan har ba'a iya cimma sulhu ba cikin lumana

Ministan Harkokin Wajen Saudi Arabia ya fada jiya Litinin cewa kasashen larabawa zasu dauki "matakai da suka wajaba" kan 'yan tawayen da ake kira Houthi 'yan Shi'a a Yemen, idan ba'a cimma sulhu cikin lumana ba kan yaki da 'yan tawayen suke yi da gwamnatin shugaba Abd Rabbu Mansour Hadi ba.

Minista Saud al-Faisal, ya gayawa manema labarai a birnin Riyadh cewa, kasashen larabawa zasu yi kokarin "kare yankin daga duk wata takala", daga nan yayi Allah wadai kan abunda ya kira "shishshigin Iran a Yemen.

Ahalinda da ake ciki, ministan harkokin wajen Yemen Riad Yassin yace shugaba Hadi ya nemi taimakon kasashen da suke yankin Gulf su dauki matakin soja kan 'yan tawayen na Houthi wadanda suka kama babban birnin kasar, Sana'a cikin watan Satumban bara, kuma yanzu suka doshi kudanci zuwa Aden inda shugaba Hadi yake. Shugaban ya tsere daga Sana'a inda 'yan tawayen suka yi masa daurin talala cikin watan jiya.

Ministan harkokin wajen ya gayawa manema labarai a Saudiyan cewa "bamu da lokaci". Sai dai bai yi bayani kan irin matakan da aiki da karfin sojan zai kunsa ba.

Sojoji da suke biyayya ga shugaba Hadi jiya Litinin sun gwabza fada da 'yan tawayen Houthi jiya Litinin wanda aka tura zuwa ta yankin Aden din, kamar yadda aka ji da majiyoyin tsaro da suka hada da 'yan banga. Jami'an tsaro sun ce 'yan tawayen sun tura dubban mayaka zuwa kudancin kasar, sun fafata da asubahin jiya Litinin da 'yan sunni lokacinda suka doshi Aden.

'Yan tawayen na Houthi wadanda Iran take daurewa gindi sun amince zasu kafa gwamnatin daunin-iko da shugaba Hadi bayan da suka kwace ikon gwmnatinsa cikin watan Satumban bara watanni shida da suka wuce. Ranar Lahadi data gabata sun kama birnin Taiz, mai tazarar kilomita 110 arewa maso yammacin Aden.

Karin tarzoma a kasar ya tilastawa Britaniya janye sauran sojojinta na musamman da suka rage a kasar, kamar yadda wani jami'i da yake da masaniyar alamarin yayi bayani.

XS
SM
MD
LG