Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Taliban ta Dauki Alhakin Kai Harin Bama Bamai Akan Motocin Kungiyar NATO


Ayarin motocin da bam ya tarwatsa a Kabul babban birnin Afghanistan.
Ayarin motocin da bam ya tarwatsa a Kabul babban birnin Afghanistan.

A wani lamari mai ban tsoro kungiyar Taliban ta kai harin bama bamai akan ayarin motocin kungiyar NATO a lokacin da kasar Afghanistan ke fama da rikicin siyasa.

Wani dan Taliban ya kai kunar bakin wake akan ayarin jerin motocin NATO inda ya kutsa da motarsa wadda take shake da bama-bamai kana ya tayar dasu a birnin Kabul babban birnin kasar Afghanistan. Wannan kutsawar da yayi tayi sanadiyar mutuwar sojoji uku da jikata wasu da dama da lalata kusan duk motocin. Duk sojojin da suka rasa rayukansu 'yan kasashen waje ne.

Idan ba'a manta ba yau kimanin watanni biyar ke nan da aka gudanar da zaben shugaban kasa lamarin da ya jawo mummunar takaddama tsakanin 'yan takara biyun dake kan gaba. Har yanzu ba'a samu daidato ba duk da kokarin da Amurka tayi na ganin an kaiga masalaha. Rudanin da zaben ya haifar yasa kasar ta zama tamkar bata da shugabanci abun da ya kara karfafa 'yan Taliban da suka dade suna adawa da gwamnati irin ta yammacin turai.

Kawo yanzu kungiyar NATO ba ta bayyana kasashen sojojin ba. Kakakin ma'aikatar harakokin cikin gidan kasar Afghanistan, Sediq Sediqi ya kara da cewa wasu fararen hula goma sha uku sun ji ciwo.

Da safiyar jiya harin bama-baman ya faru akan babban titin dake tsakanin ofishin jakadancin Amurka da filin saukar jirgin saman birnin Kabul.

'Yansanda sun ce dan kunar bakin waken ya kai harin ne kusa da babbar kofar shiga ofishin jakadancin Amurka.

Ba tare da bata lokaci ba 'yan Taliban suka fito suka yi ikirarin su ne suka kai harin.

XS
SM
MD
LG