Jumma’a, Satumba 04, 2015 Karfe 22:02

Labarai / Sauran Duniya

Kungiyar Muslim Brotherhood Tace An Amince Da Sabon Kundin Tsarin Mulkin Misira

Mata Suna Zanga Zanga a Misira
Mata Suna Zanga Zanga a Misira
Kungiyar Muslim Brotherhood ta kasar Misira tace masu kada kuri’a sun amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar da ake takaddama a kai.

Bisa ga cewar kungiyar, kashi 64% na masu kada kuri’ar sun amince da daftarin tsarin mulkin.

Muslim Brotherhood tsohuwar jam’iyar shugaban kasar Misira Mohamed Morsi tana goyon bayan sabon kundin tsarin mulkin. Sai dai kungiyoyi masu sassaucin ra’ayi da wadanda basu hada harkokin siyasa da addini da kuma Kirista suna fargaban cewa zai tauye hakinsu, sabili da zai matsanta amfani da shari’ar Islama, yayinda kuma ba a ambaci hakkin mata ba a sabon kundin tsarin mulkin.

Wani kwamitin da ya kunshi galibi ‘yan kungiyar kishin islama ne ya amince da daftarin kundin tsarin mulkin bayanda membobin kwamitin Kirista da kuma masu sassaucin ra’ayin suka janye daga zaman bisa zargin cewa, ana watsi da   ra’ayoyinsu.

An kada zagayen farko na kuri’un ne ranar 15 ga watan Disamba yayinda aka gudanar da na biyu jiya sabar.

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti