Jumma’a, Satumba 04, 2015 Karfe 22:02

Labarai / Sauran Duniya

Kungiyar Taliban Ta Dauki Alhakin Harin da aka kai Sansanin Sojojin Birtaniya a Afghanistan

Wani sojan Amurka yana sintiri inda mayaka suka kai hari a AfghanistanWani sojan Amurka yana sintiri inda mayaka suka kai hari a Afghanistan
x
Wani sojan Amurka yana sintiri inda mayaka suka kai hari a Afghanistan
Wani sojan Amurka yana sintiri inda mayaka suka kai hari a Afghanistan
Kungiyar Taliban ta dauki alhakin harin da aka kaiwa sansanin sojojin Birtaniya a Afghanistan da ya yi sanadin kashe mayakan ruwan Amurka biyu.

Kakakin kungiyar ya bayyana yau asabar cewa, harin martani ne dangane da silman da aka hada a Amurka, da ya yiwa annabi Mohammadu batanci, kuma sabili da yariman Birtaniya Harry yana aiki a sansanin.

Kungiyar tsaro ta NATO tace mayakan sun kutsa cikin sansanin Baston dake lardin Helmand jiya asabar da dare suka kai hari a sansanin ta wajen amfani da kananan makamai, da roka da kuma ‘yan kunar bakin wake.

Kungiyar NATO tace, mayaka 18 suka mutu a harin yayinda aka jiwa daya rauni aka kuma kama shi. An jiwa dakarun kasa da kasa da dama rauni.

Jami’ai sun ce Yarima Harry wanda shine na uku a matsayin sarautar Birtaniya, bai shiga wani hadari ba. An tura shi aiki a sansanin ne a matsayin matukin jirgi mai saukar angulu. Kungiyar Taliban ta yi alwashin kashe shi.

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti