Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwararru A Wani Babban Taro A Washington Sun Ce Amfani Da Karfi Kadai Ba Zai Magance Ta'addanci Ba


Taron Kirista da Musulmi na jaddada zaman lafiya
Taron Kirista da Musulmi na jaddada zaman lafiya

A cigaba da lalubo karin hanyoyin tabbatar da zaman lafiya a sassan duniya, wani taron da aka yi kwana da kwanaki ana yi a birnin Washigton, ya lura cewa dole a shiga amfani da wasu hanyoyin da ba na soji ba muddun ana so a kawar da ta'addanci a duniya.

Kwararru sun sake jaddada cewa amfani da karfi ba shi ne mafita mafi inganci ba a yakin da ake yi da ta’addanci da sauran nau’ukan tashe-tashen hankula a Nijeriya da ma duniyar baki daya.

Wani taron da wakilan kungiyoyin rajin tabbatar da zaman lafiya daga sassa dabandaban na duniya da aka yi a birnin Washington DC, ya lura cewa banda amfani da karfi, akwai kuma bukatar amfani da hanyar da ba ta soji ba wajen shawo kan matsalolin tashe-tashen hankula a duniya. Hasalima, hanyar lalamar ta fi kowacce inganci, a cewar wadanda su ka wakilci Nijeriya a wurin taron, wato Imam Nuraini Ashafa da Rabaran James Wuye.

Su ka ce bayan musayar ra’ayi da darasin da mahalarta taron daga kasashe dabandaban su ka yi, sun lura cewa dole ne a shiga amfani da wasu dabaru na hana yaduwar manufofin tashin hankali tun kafin su auku. Su ka ce karkatar da hankalin jama’a daga bakar aniya ta fi amfani da karfin bindiga wajen hana su.

Rabaran Wuye da Imam Ashafa, wadanda manyan jami’ai ne a wata kungiyar wanzar da zaman lafiya da sasanta bangarorin da ke takaddama wadda ke garin Kadunan Nijeriya, sun ce da zaran sun isa Nijeriya za su shiga amfani da hanyoyin sadarwar zamani wajen yada abubuwan da suka koya wurin taron da su ke ganin za su amfani ‘yan Nijeriya.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG