Talata, Mayu 26, 2015 Karfe 16:39

Kiwon Lafiya

Kwararru sun gano cewa yiwa mutane da dama rigakafi yana iya kare wadanda basu samu rigakafi ba

Ana yi ma dan jariri rigakafiAna yi ma dan jariri rigakafi
x
Ana yi ma dan jariri rigakafi
Ana yi ma dan jariri rigakafi
Mazu bincike sun gano cewa, yiwa mutane da dama rigakafin kamuwa da wata cuta a wuri guda yana kare sauran mutanen dake cikin al’ummar.

Bisa ga cewar kwararru, cutar da ake yadawa ta wajen jima’I da ake kira a takaice da turanci HPV tana kama kimanin kashi casa’in bisa dari na mutanen da suke jima’I a duk fadin kasashen duniya, kwayar cutar ce kuma sanadin kimanin cutar sankaran mara dari biyar kowacce shekara, da kuma mutuwar kimanin mutane dubu 290.

Wadansu nau’in kwayar cutar biyu HPV 16  da 19 sune sanadin kashi 70 bisa dari na  sankaran mara hadi kuma da sankaran hakori da na gaban mace da kuma mafitsarar namiji. Kwararru sun ce nauyin cutar HPV 6 da 11 sune sanadin kashi casa’in bisa dari na kurajen gaban mutum.

An samar da wata allurar rigakafi mai inganci dake maganin wadannan nau’in kwayar cutar duka hudu a cikin shekaru biyu da suka shige. Jami’an aikin magani sun bada shawarar a yiwa samari da ‘yan mata da kuma maza da mata da basu kai ga yin jama’I ba rigafi domin kada su kamu da kowanne nau’in kwayar cutar.

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti