Litinin, Agusta 31, 2015 Karfe 20:46

Labarai / Sauran Duniya

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da gwajin makamin Nukiliya da Koriya ta Arewa tayi.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice.Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice.
x
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice.
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice.
Aliyu Imam
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da gwajin makamin Nukiliya da Koriya ta Arewa tayi na baya bayan nan, daga nan yace zai fara aiki ba tare da bata lokaci ba kan “matakai da suka da ce” zaman martani kan wannan mataki daga koriya ta Arewa.

Pyongyang ta tabbatar da cewa ta gudanar da gwajin Nukiliya karo na uku a ranar talatan nan. Wannan mataki da ta dauka ta yi kunnen uwar shegu ga dukkan kudurorin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya, nan da nan kuwa shirin  ya janyo mata tofin Allah tsine daga Amurka, koriya ta kudu, China,  da kuma wasu kasashe.

Ministan harkokin wajen koriya ta kudu, Kim Sung-hwan, kasar da ahalin yanzu take rike da shugabancin kwamitin sulhu na karba a karba cikin watan nan, yana majalisar dinkin duniya domin ya jagoranci wani zaman kwamitin a ranar talatan nan. Ya gayawa manema labarai cewa bayan wani taron gaggawa na kwamitin da safiyar talatan kan gwajin makamin nukiliyar, cewa, gwajin makami mai cin dogon zango da Pyongyang ta gudanar  a baya bayan ya zama kalubale ga kasa da kasa kuma barazana ce ga tsaro da zaman lafiya da ba za lamunta dashi ba, a makurdin koriya da kuma yankin arewa maso gabashin Asiya.

“Koriya ta arewa ce za’a azawa duk sakamakon wannan mataki na neman talaka’ inji Mr. Kim. Y kara d a cewa kasarsa zata yi aiki da  sauran kasashe sosai wajen ganin an dauki “dukkan matakai da  suka dace” da  zasu sa Koriya ta Arewa ta jingine shirin nukiliyarta.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti