Laraba, Mayu 04, 2016 Karfe 08:55

  Labarai / Kiwon Lafiya

  Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a kara maida hankali a yaki da zazzabin cizon sauro.

  Ana yi ma dan jariri rigakafin zazzabin cizon sauroAna yi ma dan jariri rigakafin zazzabin cizon sauro
  x
  Ana yi ma dan jariri rigakafin zazzabin cizon sauro
  Ana yi ma dan jariri rigakafin zazzabin cizon sauro
  Manyan jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun jadada bukatar kara maida hankali a yunkurin kawar da cutar kanjamau, suka kuma ce ana bukatar musamman a fadada ayyukan yaki da cutar da kuma kudaden da ake kashewa a wannan yumurin.

  Shugaban babban zauren majalisar Nassir Abdul’aziz Al-Nassir ya  bayyana a wani jawabi cewa, tilas ne su dauki kwararan matakai bisa la’akari da matsayin kasashen duniya na kawar da cutar daga doron kasa.

  Mr. Al-Nssir ya bayyana cewa, ana samun ci gaba a wannan yunkurin kasancewa an sami raguwar wadanda ke kamuwa da cutar a kasashen da cutar tafi yawa, da kuma tsakanin matasa a duniya baki daya. Yayinda ake kuma samun ci gaba wajen samar da magunguna ga wadanda ke dauke da cutar.

  Bisa ga cewarsa, tilas ne a tabbatar da cewa, an cika alkawuran da aka dauka domin a daina yada cutar  a kuma magance bukatar kashe kudi domin yaki da cutar nan gaba.
  Membobin Majalisar Dinkin Duniya sun yi alkawarin daukar matakan shawo kan yaduwar HIV da nufin kawar da cutar da tayi sanadin mutuwar sama da mutane miliyan dari daga lokacin da cutar ta bulla shekaru 30 da suka shige.

  Watakila Za A So…

  Sauti Albani akan sugabancin Buhari

  Marigayi Shaikh Muhammad Awal Albani ya yi furuci akan shugabancin Buhari tun kafin ma a zabeshi, abun da yau ya zama tamkar duba Karin Bayani

  Nasarar Trump a Indiana ta sa Cruz janyewa daga takarar shugaban kasa a jam'iyyar Republican

  Senata Ted Cruz, mai wakiltar jihar Texas a majalisar dattawan Amurka ya janye daga takarar shugabancin Amurka, bayanda attajirin nan Donald Trump yayi masa mummunar kaye a zaben fidda gwani da aka yi a jihar Indiana, jiya Talata. Karin Bayani

  'Yan jarida na fuskantar barazana ga aikinsu da rayuwarsu a Sudan ta Kudu

  Jiya Talata da aka yi bikin ranar 'yan jarida ta duniya rahotanni sun nuna cewa Sudan ta Kudu ita ce kasa ta 140 cikin 180 a duniya kan 'yancin aikin jarida musamman wurin neman tantance labari daga jami'an gwamnati Karin Bayani

  Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai zauna yau akan rikicin Syria

  Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD zai zauna yau da rana domin ya saurari bayanai dangane da halin da ake ciki a Syria, bayan da aka kwashe mako da barkewar sabuwar tarzoma, musamman a birnin Aleppo,birni na biyu a kasar. Karin Bayani

  Farmakin ISIS kan kurdawa a Iraqi ya halaka jami'in sojin Amurka daya

  Amurka da kawayenta suna tsammanin irin farmakin da mayakan ISIS suka kaddamar jiya Talata a a rewacin Iraqi, suka wargaza kan mayakan kurdawa da ake kira Peshmerga na wani dan gajeren lokaci, al'amari da ya janyo mutuwar sojan Amurka na musamman daya. Karin Bayani

  Sauti PDP ta kira gwamnatin APC dake mulkin Najeriya ta sake salon tafiya

  Babbar jami'yyar adawa a Najeriya PDP na ganin babu wani abun a zo a gani da gwamnatin APC tayi tunda ta kama mulkin kasar cikin shekara daya da ta wuce idan aka kwatanta da kalamun shugaba Buhari yainda yake fafutikar neman zabe Karin Bayani

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shrin Safe
   Minti 30

   Shrin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye