Talata, Yuni 30, 2015 Karfe 22:24

Afirka

Majalisar Mulkin Wucin Gadi Ta Libya Ta Mika Mulki

Mustafa Abdel Jalil, shugaban majalisar mulki ta wucin gadin, ya mika ragamar mulki ga zababbiyar majalisar dokoki ta kasa daren laraba a Tripoli

Shugaban majalisar mulkin wucin gadi, Mustafa Abdel Jalil (dama) yana gaisawa da firayim ministan zamanin yaki,Mahmoud Jibril 8 Agusta 2012
Shugaban majalisar mulkin wucin gadi, Mustafa Abdel Jalil (dama) yana gaisawa da firayim ministan zamanin yaki,Mahmoud Jibril 8 Agusta 2012

Article Poll

Zaben lokutan da
Majalisar mulkin wucin gadi ta kasar Libya ta mika mulki cikin lumana ga majalisar dokokin kasar ta farko da aka taba zaba.

Mustafa Abdel Jalil, shugaban majalisar mulki ta wucin gadin, ya mika ragamar mulkin kasar ga mutum mafi yawan shekaru cikin zababbiyar majalisar, Mohammed Ali Salem, a wurin bukin da aka gudanar cikin daren laraba a wani hotel na birnin Tripoli.

Abdel Jalil yace daga yanzu, wannan majalisa wadda ake kira Babbar Majalisa ta Kasa, ita ce halaltacciyar wakiliyar al’ummar kasar Libya.

Majalisar da aka zaba ta kunshi kujeru 120 na masu zaman kansu da kuma wasu kujeru guda 80 da aka ware don jam’iyyu. Gungun jam’iyyu masu sassaucin ra’ayi dake goyon bayan firayim minista na lokacin yaki Mahmoud Jibril, sune suka fi taka rawa a zaben na watan da ya shige, inda suka samu kujeru 39.

A yanzu dai wannan majalisa mai wakilai 200 ita ce zata nada sabon shugabanta tare da yin jagorar kasar Libya zuwa ga cikakken zaben majalisar dokoki ta dindindin, a bayan an zana sabon daftarin tsarin mulki.
An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: Abdallah ben sidi Daga: Tchinta baraden a jahar Tahaua
09.08.2012 07:24
muna taya yan uwammu na kassar libya murnar halatacen mulkin da suka zaba da kansu.
Kai kuma sabon shugaban libya da ftn za ka yima mutanen kassarka abinda suke so gareka inko ka kuskure kaga yadda aka yima ghadafi

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti