Alhamis, Satumba 03, 2015 Karfe 20:10

Labarai / Sauran Duniya

Masana Taurari Sun Gano Wani Babban Kogi A Duniyar Taurari

Hoton nan na tauraruwar Titan dake Duniyar Saturn da kumbon Cassini na Turai ya dauka.Hoton nan na tauraruwar Titan dake Duniyar Saturn da kumbon Cassini na Turai ya dauka.
x
Hoton nan na tauraruwar Titan dake Duniyar Saturn da kumbon Cassini na Turai ya dauka.
Hoton nan na tauraruwar Titan dake Duniyar Saturn da kumbon Cassini na Turai ya dauka.
Kumbon kasa da kasa da ake kira Cassini da yake gewaya duniyar Saturn da taurarinta tun 2004, ya aiko da bayanai dalla-dalla masu muhimmanci  na wani kogi shigen kogin Nilu a kan wata tauraruwar da take kan duniyar ta  Saturn. Kogin yana da tsawon kilomita dari hudu daga inda  ya samo asali, kuma ya kare cikin wani teku.

Hukumar binciken sararin samanaiya ta turai tace wannan ne karo na farko da masana taurari suka ga siffar kogi mai girma haka a wani wuri ba a doron kasa ba.

Masana kimiyya suka ce kogin yana cike da wani sindari mi shigen ruwa  kamar yadda ya fito cikin wata na’ura mai karfi na hangen nesa da alamar baki baki a duk tsawon kogin, da ya nuna samansa yana nan sumul.
An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: ibrahim muhammad garba Daga: Abuja
16.12.2012 11:03
allah mai mai girma ,wannan ya nuna cewa Allah ne kawai masanin sirrin rayuwar mutum a bayan wannan tauraro da ke wannan makeken sarari na subahana, daga ina yake ? ina ya dosa ? da sauran tambayoyi da ke da'alaka da wannan suddabaru mai suna rayuwa. ku ci gaba da bincike masana,. mai nema na tare da cimma burinsa.

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti