Jumma’a, Afrilu 29, 2016 Karfe 07:01

  Labarai / Afirka

  Masu Fama Da Cutar Kanjamau Sun YI Zanga Zanga A Zimbabwe

  Wata mace da danta masu fama da cutar kanjamauWata mace da danta masu fama da cutar kanjamau
  x
  Wata mace da danta masu fama da cutar kanjamau
  Wata mace da danta masu fama da cutar kanjamau
  Jami’an kungiyar  masu fama  da cutar kanjamau (HIV AIDS) a kasar Zimbabwe sun nemi  Gwamnatin Zimbabwe tayi bayanin abinda tayi da milyoyin Dalolin kudin  bada tallafi da agajin masu dauke da cutar (AIDS) da aka tara.

  Daruruwan wadanda ke fama da cutar Kanjamau (AIDS) a Zimbabwe cikin rigunan Sigiletin dake dauke da kalmomin “HIV POSITIVE” suka yi jerin gwano a kan titunan birnin Harare zuwa ofishin kula da hana yaduwar cutar AIDS a Zimbabwe.

  Douglas Muzanenhamo, daya daga cikin shugabannin masu zanga-zangar ya  bayyana cewa,

  “Tuntuni mun shaidawa Gwamnatin Zimbabwe bukatarmu ta neman a rika bayyana mana abinda ake yi da kudaden da ake karba da sunan agajin wadanda ke dauke da cutar kanjamau,a kuma rika samar mana magunguna a kan lokaci, don haka muka ga yanzu ya zama dole muyi tattaki zuwa ofishin dake kula da wadannan kudaden agajin domin bayyana masu cewar muna matukar bukatar magunguna”.

  Kasar Zimbabwe dai na daga cikin kasashen da cutar kanjamau (AIDS) tafi yiwa illa duk da cewar da alamar illar da cutar keyi ta fara raguwa a kasar. ‘Yan sandan Zimbabwe sun ce ba zasu hana gudanar da zanga-zangar ba, ba kuma zasu taba kowa ba, amma duk da haka shugabannin gangamin sun nace kan sai lallai sunga alamar Gwamnatin Zimbabwe ta saurari kukansu. 

  Daya daga cikin masu  zanga-zangar Chabikwa yace

  “ai daman hakkin ‘yan Zimbabwe ne suyi zanga-zangar nuna kyamar abinda zai cutar dasu, domin kundin tsarin mulkin Zimbabwe ya tanadar da hakan, muna yin zanga-zangar ne ba domin nuna kiyayya ga Gwamnatin Zimbabwe ba, muna yi ne domin yaki da matsalar cin hanci da karbar rashawa dake janyo mana cikas a halin zaman rayuwar mu”.

  Sauti

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye