Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matar Kakakin Majalisar Dokokin Kasar Nijer a Cikin Abun Fallasa


Wasu jarirai sabbin haihuwa.
Wasu jarirai sabbin haihuwa.

Rade-radin cewa wasu manyan jami'an kasar Nijer na sayen jarirai daga Najeriya, ya tabbata gaskiya, tuni har kotu ta iza keyar mutum 18 gidan kaso.

Kamar almara, kamar tatsuniya lokacin da aka fara baza jita-jita da rade-radi a kasar jamahuriyar Nijer cewa wasu kusoshin kasar sun sayi jarirai daga Najeriya sun yi musu takardun shaidar zama 'yan kasa na jabu sun mayar da su tamkar 'ya'yan da suka haifa da cikin su, amma sai ga shi wannan magana ta zama gaskiya.

Da tsakar daren jiya da misalin karfe biyu ne wata kotun da ke birnin Niamey ta yanke hukuncin dakatar da wasu mutanegoma sha takwas da ake zargi da yin fataucin jarirai daga kasar Najeriya suna shiga da su Nijer domin yi musu takardun jabu da maida su 'ya 'yan su a kasar ta Nijer.

Daga cikin wadanda kotun ta dakatar har da matan tsoffin darektocin hukumomin kasar da matan ministoci da ma matar kakakin majalisar dokokin kasar ta Nijer Hama Amadou. Wakilin sashen Hausa a birnin Niamey Abdoulaye Mamane Amadou ya aiko karin bayani a cikin wannan rahoto:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tun a cikin watan janairu jaridar l'Evenement ta bankado labarin wanda da farko aka yi watsi da shi, daga bisani babban editan jaridar Moussa Aksar ya kwashi 'yan sandan ciki na kasar Nijer suka yi tattaki har kudancin Najeriya inda ke da wuraren da ake cinikin jarirai.

Masu cinikin jarirai sun nuna musu shaidar sunayen manyan jami'an kasar Nijer maza da mata da suka sayi jarirai fiye da dari. Har wa yau an ba su sunayen fataken jariran da kuma direbobin da ke shigi da fici da su daga kasar Nijer zuwa kudancin Najeriya.

Lauyan da ke kare wasu daga cikin mutanen goma sha takwas da aka iza keyar su zuwa gidan kaso, maitre Souley Oumarou ya ce hukumomin Najeriya ne ya kamata su kama masu cinikin jariran, su kai su Nijer, su, su nuna wadanda suka sayi jarirai a hannun su, ya ce ba hukumomin Nijer ba ne ya kamata su kama 'yan kasar Nijer su tsare su a kan wannan batu.

XS
SM
MD
LG