Alhamis, Fabrairu 11, 2016 Karfe 13:54

  Labarai / Najeriya

  Matsalar Rashin Siginal Na Wayar Salula A Najeriya

  Wasu 'yan Najeriya, musamman a Maiduguri, sun ce kamar su na kurkuku don ba su iya kira ko karbar kira a wayoyinsu.

  x
  Makonni da dama a bayan da kungiyar Jama'atu Ahlus Sunnati Lidda'awati Wal Jihad, wadda aka fi sani da sunan Boko Haram, ta dauki alhakin kai hari a kan wasu cibiyoyin sadarwa na wayoyin salula a sassan kasar, mazauna wasu daga cikin wuraren da abin ya shafa sun ce ji suke yi kamar su na kurkuku, inda wayoyinsu ab su aiki yawancin lokuta, kuma ba su da hanyoyin shiga Intanet.

  Wakiliyar Muryar Amurka Heather Murdock ta ce idan mutum yayi kokarin kiran wasu jihohin arewacin Najeriya daga Abuja, musamman wadanda ke yankin arewa maso gabas, yawancin abinda zai ji shi ne sakon cewa ko dai wayar tana kashe, ko kuma ya ji kamar ana amfani da wayar.

  Wani wakilin Muryar Amurka a Maiduguri ya ambaci mazauna birnin su na kukar cewa harkokinsu na kasuwanci sun fara ja da baya, kuma sun fara fargabar cewa wannan abu zai kai su ga talaucewa ganin da ma dai ba wani karfi suke da shi ba.
  Gawarwaki na wadanda ake zaton 'yan Boko haram ne a kusa da wata motar 'yan sanda a Maiduguri, ranar 31 ga watan Yulin 2009, lokacin mummunan gumurzun da aka yi a tsakanin jami'an tsaro da 'ya'yan kungiyar.Gawarwaki na wadanda ake zaton 'yan Boko haram ne a kusa da wata motar 'yan sanda a Maiduguri, ranar 31 ga watan Yulin 2009, lokacin mummunan gumurzun da aka yi a tsakanin jami'an tsaro da 'ya'yan kungiyar.
  x
  Gawarwaki na wadanda ake zaton 'yan Boko haram ne a kusa da wata motar 'yan sanda a Maiduguri, ranar 31 ga watan Yulin 2009, lokacin mummunan gumurzun da aka yi a tsakanin jami'an tsaro da 'ya'yan kungiyar.
  Gawarwaki na wadanda ake zaton 'yan Boko haram ne a kusa da wata motar 'yan sanda a Maiduguri, ranar 31 ga watan Yulin 2009, lokacin mummunan gumurzun da aka yi a tsakanin jami'an tsaro da 'ya'yan kungiyar.


  Maiduguri dai ita ce cibiyar kungiyar Boko Haram, wadda a kwanakin baya ta yi ikirarin cewa ta kai hare-hare kan turakan kamfanonin salula a garuruwa da dama a saboda tana zarginsu da laifin taimakawa gwamnati wajen bin sawun 'ya'yanta da ake kamawa.

  Kamfanonin sadarwa na wayar salula a Maiduguri, sun yi alkwarin gyara turakan, amma sun roki jama'a da su kara nuna hakuri. Sai dai kuma wani ma'aikacin kamfanin salula da ya nemi kada a bayyana sunansa, yace ma'aikatan da ya kamata su yi wannan gyara sun ki yi saboda fargabar cewa za a kai musu farmaki lokacin da suke aikin.

  Da yawa daga cikin ma'aikatan ma sun gudu sun bar Maiduguri.

  Jami'an tsaro sun yi alkawarin kara yawan 'yan sandan da zasu yi gadin cibiyoyin sadarwa. Amma a Najeriya, su kansu sojoji da 'yan sandan kasar, kamar kowa ma, sun dogara ne a kan wayoyinsu na salula domin sadarwa, tunda layukan tarho na kasa sun lalace.

  Watakila Za A So…

  Shirin Hantsi

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku.
  Shirin Safe

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu na gabatar da wasu shirye-shirye kamar Noma da Lafiya Uwar Jiki.
  Shirin Dare

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na yadda duniyar ta yini da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu kan bude muku layuka domin ku bugo ku bayyana mana ra’ayoyinku kan batutuwan da suka fi muhimmanci a wannan rana, ko kuma wadanda ke ci muku tuwo a kwarya.
  Shirin Rana

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai da dumi-duminsu daga kowace kusurwa ta duniya, musamman ma dai muhimman abubuwan da suka faru, ko suke faruwa a kusa da ku a wannan rana.

  An rufe wannan dandalin
  Yadda Ake Son Gani
  Sharhi/Ra'ayi
       
  by: haruna Daga: jeddah
  21.09.2012 19:24
  Allah yabamu zaman lafiya a nigeria.

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye