Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan ISIS Suna dada Kutsawa Cikin Yankin Kurdawa a Kasar Syria


A polling station in the Kamwokya neighborhood of Kampala, Uganda, saw a low turnout during local elections, with only a fraction of those registered arriving to vote, Feb. 24, 2016.
A polling station in the Kamwokya neighborhood of Kampala, Uganda, saw a low turnout during local elections, with only a fraction of those registered arriving to vote, Feb. 24, 2016.

Kungiyar ISIS tana cigaba da fadada yankunan da take kamawa tare da kara kutsa kai cikin yankin Kurdawa dake kasar Syria inda suka kwace garuruwa da kauyuka da dama.

Mayakan kishin Islama da ake kira ISIS suna kara kutsawa arewacin Syria, inda suke mamaye garuruwan Kurdawa da dama a wani yunkurin da zai iya karawa kungiyar karfin iko a kan iyakar Turkiya.

Da yake hira da sashen Kurdawa na Muryar Amurka, wani dan jarida ya tabbatar da cewa jama’a da dama suna kauracewa yankin.

Mayakan sun tilastawa kimanin mutane dubu dari zuwa gudun hijira a Turkiya tun ranar Jumma’a. Jami’an tsaron kasar Turkiya sun dauki matakin wucin gadi tare da rufe hanyoyin shiga kasarm yayin da suna kuma amfani da mesar ruwa da barkokon tsohuwa wajen tarwatsa dandazon mutanen da suka taru a bangaren Turkiya jiya Lahadi.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG