Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministoci da Hafsan Hasoshin Kasashen dake Anfani da Tafkin Chadi Zasu Yi Taro


Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar
Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar

Cikin shekaru biyu ministoci da hafsan hafsoshin kasashen dake anfani da tafkin Chadi sun yi taro sau hudu akan matsalolin tsaro musamman tashin tashinar da kungiyar Boko Haram ke haddasawa

Abun da yafi cima kasashen tuwo a kwarya shi ne yakin sunkuru musamman irin wanda kungiyar Boko Harama ke gudanarwa.

A taron karshe da ministoci da hafsan hafsoshin kasashen suka yi a birnin Niamey babban birnin Jamhuriyar Niger a watan Yuli da ya gabata, kungiyar ministocin da hafsan hafsoshi ta yanke shawarar kafa wata bataliya ta sojoji mai kunshe da sojojin kasashe shida domin kare iyakokin kasashen tare da dakile ta'adanci irin na Boko Haram.

Ministan harkokin tsaron kasar Niger ya jagoranci taron. Yace tarukan da suka yi can baya sun basu daman kafa wata bataliya ta musamman. Amma duk da yanke shawarar abokan gaba na samun cigaba tare da nuna masu cewa har yanzu akwai sauran runa a kaba. Ya kira a hanzarta a dinke abubuwan da suka saura domin kafa bataliyar. Kamata yayi a yi gaggawa domin mutanen dake cikin wahalar 'yan ta'ada sun tagayyara. Kamata yayi a karshen taron a ce matakin kafa bataliyar ta tabbata da kuma samar da mahimman kayan aikin da suka cancancesu a cikin dan lokaci kalilan.

Daga cikin abubuwan dake kawo cikas ga batun kafa bataliyar domin yaki da 'yan Boko Haram har da batun shiga kasar Kamaru cikin shirin gadan gadan. Tun farko kasar Kamaru ta dauki alkawarin aika sojoji 700 amma daga bisani 300 suka isa. Banda haka akwai kudaden da rundunar ke bukata.

Injiniya Sanusi Imrana Abdullahi sakataren zartaswa na hukumar tafkin Chadi yace suna bukatar su samu cikakken hadin kan Kamaru ta shigo gaba gadi domin a yi tafiyar sosai. Akwai kuma harkokin gudanarwa na sarafa kudi.

Yau ministocin zasu sake taruwa a Niamey su tattauna akan batun tafkin da kuma yaki da kungiyar Boko Haram. Cikin wadanda zasu halarci taron na yau har da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da kuma takwaransa na kasar Kamaru, kasar da ita ma tana fama da barazanar 'yan Boko Haram.

Ga rahoton Abdullahi Mamman Ahmadu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG