Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ministocin harkokin wajen kasashe uku sun tattauna akan matsalar ta'adanci a yankin Sahel


Firayim Ministan Nijar, Brigi Rafini wanda ya kasance a wurin taro kasashen uku
Firayim Ministan Nijar, Brigi Rafini wanda ya kasance a wurin taro kasashen uku

Tattaunawar kasashen uku wato Jamus da Faransa da Nijar wacce aka yi tare da halartar Brigi Rafini firayim ministan Nijar din ta ba bangarorin damar gayawa juna gaskiya akan matsalolin dake uma'luba'isan tashe-tashen hankula a yankin Sahel

Sun kuma tattauna matsalolin dake kawo kwararar matasa zuwa Turai ta barauniyar hanya.

Daga bisani ministocin harkokin wajen kasashen uku suka kira taron manema labarai na hadin gwuiwa.

Ministan harkokin wajen Nijar Ibrahim Yakubu yace sun yi lissafi kowace shekara mutane sun kai dubu dari dake ratsawa cikin Nijar domin su tsallaka zuwa Turai. Yace sun fada masu cewa idan har mutum ya bar kasarsa to akwai matsala. Ba banza kawai zai bar kasarsa ba. Akwai talauci. Akwai yunwa. Akwai kuma rashin kwanciyar hankali.

Idan ana son a magance matsalar to sai su taimakawa kasar Nijar wadda take bukatar kudi miliyan 660 na sefa.

Ministan yace yanzu ma sun taimaka da kudin Euro miliyan 75 a kokarin rage matsalolin.

Akan yaki da ta'adanci yace kodayake karfin Boko Haram ya ragu amma har yanzu yakin na nan. Saboda haka yakamata a tsaya daram a cigaba da yakin.

Har yanzu ana haifar ta'adanci a Mali kana a yadashi yankin kasashen Sahel.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG