Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musulmi sun gudanar da zanga zangar kyamar batancin da aka yiwa annabi Muhammadu


Wasu masu zanga zanga a kofar ofishin jakadancin Amurka na birnin Bangkok
Wasu masu zanga zanga a kofar ofishin jakadancin Amurka na birnin Bangkok
‘Yan sanda da masu zanga zanga sun yi arangama yau asabar a Bangladash yayin wata sabuwar zanga zanga da ta biyo bayan silman da aka yayata a hanyar sadarwar internet ana yiwa annabi Muhammadu ba’a.

Jami’an tsaro sun harba barkonon tsohuwa a Dhaka babban birnin kasar, da nufin tarwatsa daruruwan masu zanga zanga dake jifa da duwatsu, da suka kunshi gamayyar wadansu kungiyoyin addinin Islama 12.

Shaidu sun ce masu zanga zangar sun kona ababan hawa da suka hada da motar ‘yan sanda. An kama wadansu daga cikin masu zanga zangar.

Gamayyar kungiyar da ta jagoranci zanga zangar ta yi kira da a gudanar da yajin aiki na kasa gobe lahadi domin nuna kyamar bidiyon da aka hada a Amurka.

A Najeriya, dubban mutane dake nuna kyamar hoton bidiyon sun yi zanga zanga a kan titunan Kano, birni mafi girma a arewacin kasar da Musulmi suka fi rinjaye . Masu zanga zangar sun yi jerin gwano zuwa kan titin da ya nufi fadar sarkin Kano.

An gudanar da zanga zangar ne kwana daya bayanda aka kashe a kalla mutane 17 a wata arangama tsakanin jami’an tsaro da masu zanga zanga a Pakistan.

Dubban Musulmi sun kuma gudanar da zanga zanga jiya jumma’a a wadansu kasashe da suka hada da Afghanistan, India, Sri Lanka, Bangladesh, Iran, Lebanon da kuma Indonesiya. Wadansu masu zanga zangar sun kona tutocin Amurka da kuma mutum-mutumin shugaban Amurka Barack Obama.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG