Jumma’a, Nuwamba 27, 2015 Karfe 11:01

Labarai / Sauran Duniya

Mutane 80 Suka Mutu A Yunkurin Ceto Ma'aikatan Kamfanin Gas na Algeriya

Kamfanin gas na Algeriya
Kamfanin gas na Algeriya
Grace Alheri Abdu
Jami’an kasar Algeria sun ce garkuwa da ma’aikata da mayakan kishin Islama suka yi da kuma sumamen sojan da aka kai a masana’antar iskar gas dake Hamada sun yi sanadin mutuwar mutane 80, da suka hada da ‘yan kasashen ketare da dama.

Jami’ai da suke binciken ginin sun gano wadansu karin gawarwaki  25 jiya Lahadi, sai dai sun ce jikunansu sun yi kaca kaca, yana da wuya a tantance ko mayaka ne ko kuma wadanda aka yi garkuwa da su ne.

Mayakan kasar Algeriya sun kama mayaka biyar da rai lokacin da suka kai sumamen.

Kamfanin dillancin labaran kasar Algeria yace mayakan sun kashe mutane bakwai daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su lokacin da aka kai sumamen, yayinda dakarun Algeriya suka kashe mayakan da suka yi garkuwa da su 11. An kuma kashe mayaka da wadanda aka yi garkuwa da su da dama tun farkon gumurzun, yayinda wadansu mutanen da aka yi garkuwa da su suka tsira da ransu.

Mayaka sun kwace masana’antar iskar gas ta Ain-Amena ranar Laraba.
Shugaban kungiyar mayakan kishin Islama Mokhtar Belmokhtar ya dauki alhakin kai harin. A cikin hoton bidiyo da ya buga a shafin internet jiya Lahadi, yace ya dauki wannan matakin ne da yawun kungiyar al-Qaida ya kuma bayyana cewa mayaka 40 ne daga kasashen Musulmi da na yammaci suka kai harin.
Belmokhtar yace harin martani ne kan matakin sojan da Faransa ta ke dauka a kan mayakan dake da alaka da  kungiyar al-Qaida a Mali.

Sauti

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye