Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Muhawarar 'Yan Republican a New Hamphsire


Muhawarar 'yan takara neman shugabancin Amurka a karkashin jam'iyar Republican
Muhawarar 'yan takara neman shugabancin Amurka a karkashin jam'iyar Republican

‘Yan takarar neman shugabancin Amurka a karkashin Jam’iyar Republican sun tafka muhawara a New Hampshire, wacce ta fi maida hankali kan harkokin kasashen waje, inda suka yi ta sukar junansu a daren jiya Asabar.

Wannna muhawara ta gudana ne yayin da ya rage kasa da kwanaki uku a yi zaben New Hampshire a yunkurin fitar da dan takarar da zai wakilci jam’iyar a zaben karshen shekarar nan.

Daga cikinsu dai babu wanda ya fi fusata kamar gwamnan New Jersey, Chris Christie, wanda ya yi ta caccakar Sanata Marco Rubio a farkon muhawarar, inda ya ce ba shi da kwarewar da zai iya zama shugaban kasa.

A daya bangaren kuma hamshakin attajiran nan Donald Trump, ya fi maida hankali ne akan matakan da ya ke so ya dauka game da batun bakin haure, ciki har da batun gina Katanga a kan iyakar Amurka da Mexico, kana ya ce zai maida hankali sosai wajen yaki da kungiyar ISIS.

Shi kuwa Ted Cruz wanda ya zo na farko a zaben Iwoa, cewa ya yi akwai bukatar hare-haren da ake kaiwa a Syria da Iraqi, su kasance sun maida hankali kan ‘yan ta’adda ba kowa-da-kowa ba.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG