Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben 2015: Ra'ayoyi Kan Shari'ar Gwamnoni


Gwamnonin Yankin arewa maso gabashin Najeriya
Gwamnonin Yankin arewa maso gabashin Najeriya

Biyo bayan hukunce-hukunce kotunan Najeriya kama daga na sauraron kararrakin zabe zuwa kotun koli 'yan siyasa da jama'a sun bayyana ra'ayoyinsu.

Kawo yanzu an kallama duk shari'un gwamnoni a sakamakon korafin zaben shekarar 2015 da aka yi a Najeriya.

Ba kamar yadda aka samu a zabukan 2011 ko kuma na 2007 inda aka soke zaben wasu gwamnoni. Irin ta hakan ne Rotimi Amaechi ya zama gwamnan Rivers kana Adam Oshiomole ya maye gurbin Farfasa Osunbor.

To amma a wannan karon kotun koli ta tabbatarwa duk gwamnonin nasara. Jam'iyyar PDP ce ta fi samun nasara domin babu wani gwamnanta da kotun koli bata tabbatar da zabensa ba har ma jam'iyyar na cewa sashen shari'a sashen madogara ne..

A wani bangaren kuma sakataren jam'iyyar APC Mai Mala Boni ya kira ga 'yan jam'iyyar da suka je har koli amma ba nasara da su natsu su yi da'a da yin koyi da Shugaba Buhari wannda sau tarikotun koli ta hanashi cin zabe. Ya yi hakuri, ya jajirce sai gashi yanzu ya zama shugaban kasa.

Cikin 'yan takaran gwamna na PDP da suka je kotu amma basu ci nasara ba har da na jihar Yobe Adamu Maina Waziri. Mai magana da yawunsa yace komi a barwa Allah. Haka ma dan takarar gwamnan jihar Gombe na APC yace komi ya barwa Allah.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG