Litinin, Fabrairu 08, 2016 Karfe 11:01

  Labarai / Kiwon Lafiya

  Najeriya ta kara kaimi wajen kare yara daga daukar cutar HIV

  Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa, ta kara damara domin ganin ta magance yadawa kananan yara cutar kanjamau

  Wayansu kananan yara
  Wayansu kananan yara

  Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa, ta kara damara domin ganin ta magance  yadawa kananan yara cutar kanjamau. Daya daga cikin matakan da gwamnatin ke shirin dauka shine, aiwatar da shirin Hukumar lafiya ta Duniya da ake kira “Option B Plus”.

  Darekta janar na cibiyar yaki da cutar kanjamau na kasa farfesa John Idoko ne ya bayyana haka a wajen taron yaki da cutar kanjamau na kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Washington DC.

  Gwamnati zata  dauki kwararan matakan cimma muradin karni da kuma rage yada kwayar cutar kanjamau daga uwa zuwa jariri da kimanin kashi casa’in bisa dari kafin shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, da kuma tallafawa mata masu juna biyu dake dauke da kwayar cutar kanjamau.

  Farfesa Idoko  ya bayyana cewa karancin kudi yana gurguntar da yunkurin cimma wannan burin, dalilin da kuma yasa daga cikin dakunan kula da mata masu juna biyu dubu takwas da dari uku da sittin da ake da su, dari shida da sittin kadai suke kulawa da matan dake dauke da kwayar cutar kanjamau.

  Ya kuma bayyana takaicin ganin yadda kimanin kashi 50% na mata masu juna biyu a yankunan karkara basu zuwa awo duk da kokarin da gwamnati ke yi na samar da gidajen awo a yankunan karkara.

  Watakila Za A So…

  Shirin Hantsi

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku.
  Shrin Safe

  Shrin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu na gabatar da wasu shirye-shirye kamar Noma da Lafiya Uwar Jiki.
  Shirin Rana

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai da dumi-duminsu daga kowace kusurwa ta duniya, musamman ma dai muhimman abubuwan da suka faru, ko suke faruwa a kusa da ku a wannan rana.
  Shirin Hantsi

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku.
  Shirin Safe

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu na gabatar da wasu shirye-shirye kamar Noma da Lafiya Uwar Jiki.

  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shrin Safe
   Minti 30

   Shrin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye