Alhamis, Fabrairu 11, 2016 Karfe 15:56

  Labarai / Sauran Duniya

  Shugaban Hukumar Leken Asirin Amurka Janar Petreaus Yayi Murabus...

  Helkwatar hukumar leken asirin Amurka CIA.Helkwatar hukumar leken asirin Amurka CIA.
  x
  Helkwatar hukumar leken asirin Amurka CIA.
  Helkwatar hukumar leken asirin Amurka CIA.
  Janar David Petreaus mai ritaya, mutuminda ake jijinawa wajen nasarar karkato yakin Amurka a Iraqi, yayi murabus daga mukaminsa na shugaban hukumar leken asiri na Amurka watau CIA, sabo da zina.
  Janar David Petreaus mai ritayaJanar David Petreaus mai ritaya
  x
  Janar David Petreaus mai ritaya
  Janar David Petreaus mai ritaya

  A cikin wasika da  ya rubutawa ma’aikatan hukumar CIA, Petreaus ya gaya musu cewa shi da kansa ya mikawa shugaba Obama takardarsa neman ajiye aiki ranar Alhamis. Ya kara da  cewa shi Petreaus ya yi ragwan tunani” kuma wannan ba hali ne da ya dace da mutuminda ya kasance shugaba ba.

  Tsohon janar na mayakan Amurkan, yace babban karamci ne a gareshi na aiki a hukumar CIA, daga nan ya godewa ma’aikatan hukumar saboda aiki tukuru da suke yi.
  Shugaba Obama yace ta aikinda janar Petreaus yayi dokacin rayuwarsa  a soja da kuma kasancewa shugaban hukumar leken asiri ta Amurka, ya kiyaye lafiyar Amurka, kuma ya kara karfafata.

  Kafofin yada labaran a Amurka sun bada rahoton cewa hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka FBI ce ta bankado lalatar da janar din yake yi, lokacinda take binciken wata ‘yar jarida Paula Broadwell, saboda tana kokarin samun bayanan sirri ta kafar email din janar Petreaus. ‘yar jaridar ta rubuta littafi kan tarihin rayuwar janar Petreaus, kuma rahotannin sun ce bata da shamaki zuwa gun janar Petreaus a lokacinda yake Afghanistan.

  Amma ita hukumar FBI bata ambaci Paula Broadwell  cewa itace matar da janar din yake lalata da  ita ba, shi ma janar Petreaus bai bayyana sunan matar ba.
  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye