Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Tace Ba Zata Yi Yaki da Turkiya Ba


Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov
Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei lavrov ya fada jiya Laraba cewa akwai alamun kakkabo jirgin saman yakin kasar daTurkiyya tayi, "an kitsa shine da gangan domin a takali Rasha," duk da haka Rasha ba zata yi yaki da Turkiyya ba.

Lavrov yace, al'amrin zai sa Rasha ta sake duba dangantakarta da Turkiyya. Ya soke ziyarar da ya shirya zaikai Ankara jiya Laraban, amma ya zanta da takwaran aikinsa na Turkiyya,kuma sun amince zasu gana cikin kwanaki masu zuwa.

A gefe daya kuma, ma'aikatar harkokin wajen Rashan a cikin wata sanarwa data fitar a jiyan, ta ce ministan harkokin wajen Lavrov a tattaunawar da ya yi da ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ta wayar tarho, ya gaya masa cewa da harbe jirgin saman yakin Rasha, shugabannin Turkiyya sun nuna "suna tareda ISIS."

Ahalinda ake ciki kuma, daya matukin jirgin da Turkiyyan ta harbe wanda yayi amfani da laimar tsira daga cikin jirgin yanzu ya isa wani sansanin sojin Rasha bayan da sojojin Syria suka ceto shi.

A wani lamari kuma, Jami'an tsaron Amurka sun ce suna sa ido kan rahotanni da suke nunin cewa an kai farmaki da jiragen yaki kan wata tawagar motocin ayyukan jinkai jiya Laraba, kusa da da garin Azaz dake Syria, kimanin kilomita shida kudu daga kan iyakar kasar da Turkiyya.

XS
SM
MD
LG