Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Kasar Masar Ya Cigaba


Magoya bayan Morsi dauke da akwatin gawar wani da aka kashe
Magoya bayan Morsi dauke da akwatin gawar wani da aka kashe

Rikicin kasar Masar sai cigaba ya ke yi yayin da magoya bayan Morsi suke dada fitowa zanga zanga duk da kashin kiyashin da ake yi masu

Duk da kashin kiyashin da sojojin kasar Masar ke yiwa magoya bayan hambararen shugaban kasa Mohammed Morsi dan jam'iyyar 'Yan'uwa Musulmai, sai dada fitowa suke yi suna shiga zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Abokin aiki Bello Galadanchi ya zanta da wani ganao, mazauni a kasar Masar, Ahmed Abba Majidadi Binanchi. Lamarin sai kara rincabewa ya ke yi domin yau magoya bayan hambararen shugaba Morsi da na gwamnatin yanzu sun fito zanga zanga kana jami'an tsaro sun bazu koina. Magoya bayan Morsi suna Allahh ya isa domin, injisu, an kashe masu mutane fiye da dubu uku. Suna daga tuta suna cewa gwamnatin yanzu ta kau Morsi ya dawo kan karagar milki.

Harkokin yau da kullum sun tsaya cik domin yawacin shaguna a rufe suke. Motocin haya babu su idan kuma akwai sun ninka kudi ninkin baninkin. Hatta gidanjen mai an rufesu domin fashe-fashe da aka yi. Ma'aikatu sun dena aiki domin rashin tabbas.

Babu tunanin wannan rikici zai kawo karshe nan da 'yan kwanaki domin magoya bayan Morsi sun ce mutuwa ma suke so. Don haka ana kashesu suna kara fitowa. Kamar yadda wani masanin tarihin kasar ya fada da can 'yan Jam'iyyar 'Yan'uwa Musulmi sun saba da sadakar da ransu. Sun saba da aka kullesu da kuma muzguna masu a gwagwarmayarsu da tafi shekaru hamsin suna yi da gwamnatocin kasar. Don haka wannan ba shi ne farko ba kuma zasu jaje sai dai a cigaba da kashesu.

Ga karin rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:43 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG