Alhamis, Afrilu 28, 2016 Karfe 20:48

  Labarai / Afirka

  Sabon Shugaban Somaliya Ya Tsallake Rijiya Da Baya

  'Yan harin kunar-bakin-wake har uku sun yi kokarin kai farmaki kan hotel din Jazeera Palace inda shugaban da ministan harkokin wajen Kenya suke ganawa da 'yan jarida

  Sojojin Somaliya su na tsaye kusa da gawar wani da aka ce ma'aikacin hotel din ne a hagu, wanda ya mutu bayan tashin bama-bamai biyu a kusa da kofar shiga hotel din mai suna Jazeera Palace, hedkwatar wucin-gadi ta sabon shugaban Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud.
  Sojojin Somaliya su na tsaye kusa da gawar wani da aka ce ma'aikacin hotel din ne a hagu, wanda ya mutu bayan tashin bama-bamai biyu a kusa da kofar shiga hotel din mai suna Jazeera Palace, hedkwatar wucin-gadi ta sabon shugaban Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud.
  Sabon shugaban kasar Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud, bai samu ko da kwarzane ba a lokacin da 'yan harin bam na kunar-bakin-wake suka kai farmaki a kan hotel din da yake zama.

  Ministan harkokin wajen kasar Kenya, wanda yake ziyarar Mogadishu a lokacin, yana magana da 'yan jarida tare da shugaban a cikin hotel din, sai aka ji karar tashin bam, da kuma harbe-harbe da bindiga.

  An ci gaba da wannan ganawa da 'yan jarida, inda shugaba Sheikh Mohamud ya karbi abin magana, ya ci gaba da yin jawabi ga 'yan jarida. Kwatsam sai aka ji tashin bam na biyu a wajen wannan hotel mai suna Jazeera Palace.

  Hoton bidiyo na ministan harkokin wajen Kenya yana jawabi sai aka ji tashin bam na farko

  Rundunar Tarayyar Kasashen Afirka a Somaliya, wadda take taimakawa wajen kare shugaban, ta bayar da sanarwar cewa 'yan harin kunar-bakin-wake su uku ne suka kai farmaki a kan hotel din. Ta ce an harbe biyu, bama-baman dake jikinsu ya tarwatse a lokacin da suka yi kokarin shiga harabar hotel din. An harbe na uku aka kashe shi ba tare da bam din jikinsa ya tashi ba.

  Babu ko da mutum daya dake cikin hotel din da ya ji rauni. Rundunar ta Tarayyar Afirka ta ce sojanta daya ya mutu tare da maharan su uku. Shaidu sun ce akwai fararen hular da suka rasa rayuka a kofar hotel din.

  Sa'o'i biyu a bayan tashin bama-baman, kungiuar al-Shabab ta dauki alhakin kai su cikin wani sako ta hanyar dandalin Twitter a kan Internet.

  daga bisani, an dauki sabon shugaban na Somaliya tare da tawagar Kenya da ta kawo masa ziyara zuwa wani wurin da ba a bayyana ba.

  A ranar litinin ne majalisar dokokin Somaliya ta zabi Hassan Sheikh Mohamud a matsayin shugaban kasa. Wannan zabe shi ne matakin karshe a wani shirin dake samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya na kafa gwamnatin tarayya mai dorewa a kasar Somaliya.
  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye