Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sai Nan Da Wata Daya Za'a Ji Sakamakon Zaben Nijar


Ba za'a iya jin sakamakon zaben Shugaban kasar Nijar da na 'yan Majalisu ba sai nan da wata daya bayan an sake kara zaben 'yada kanin wani tsakanin Mahamadu Issoufou da Hama Amadou, inji hukumar zaben kasar.

Har ya zuwa yanzu dai, masu zaben da suka kada kuri’unsu a jamhuriyar Nijar suna dakun jin nsakamakon zaben da aka aiwatar a makon da ya shude na shugaban kasa da ‘yan majalisu.

To sai dai kuma suna da sauran jiran da zai kai wata 1 nan gaba kafin a san wanda zai lashe zaben bayan zagaye na biyu da za a yin a zaben. Domin kuwa sakamakon da ya fito a ranar juma’ar shekaran jiya, ya nuna Shugaban kasar mai ci ya sami kaso 48 ne.

Wanda ya sa Muhammadu Issoufou din mai neman ta zarce a kan gaba. Shi kuma babban abokin adawarsa Hama Amadou yana manne da shi a baya a matsayin na biyu a zaben.

To amma kasancewa Issoufou bai kai kaso 50 daga jimillar kuri’un da aka kada ba yasa zai an yi zaben yada kanin wani. Tsohon Firaminista Hama Amadou dai yana garkame a gidan yari bisa zargin safarar jarirai.

XS
SM
MD
LG