Jumma’a, Nuwamba 27, 2015 Karfe 20:01

Labarai / Sauran Duniya

Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry Zai Fara Ziyararsa Ta Farko Zuwa KetareTun.....

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry.Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry.
x
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry.
Aliyu Imam
Sabon sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai fara ziyarar aikinsa ta farko zuwa kasashen ketare, tun bayanda ya karbi aiki daga hanun Hillary Clinton ciikin watan nan.

Ana sa ran yau lahadi zai bar Washington zuwa Ingila a rangadin kasashe tara cikin kwanaki 11.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka tace rikicin Syria zai kasance babban kan ajendarsa a tattaunawar da zai yi da jami’an kasa da kasa da zai gana da su a lokacin wannan ziyara.Haka kuma Kerry yana da niyyar ganawa da shugabannin gamayyar ‘yan hamayya na Syria.

Daga London Kerry zai nufi Berlin, da Paris, inda zai tattauna kan hadin kai tsakanin Washington da Paris da  wasu kasashe wajen baiwa Mali gotyon baa a rikici da kasar take fuskanta.

Daga nan Mr. Kerry zai kai ziyara Roma, da Turkiyya, da Masar, inda ma’aikatar harkokin wajen Amurka tace zai jaddada muhimmancin hada kai, sannan zai gana da jami’an kungiyar hada kan kasashen larabawa da nufin shawarwari kan hanyoyin tunkarar kalulable da duka sassa suke fuskanta  a yankin.

Kerry zai kammala rangadinsa a Saudiyya da Abu Dhabi, sannan ya yada zangonsa ta karshe a Qatar.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Sauti

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye