Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakatare Kerry Ya Kalubalanci Cuba Saboda Tsare Wani Ba'amarike


Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya bayyana kasar Cuba a matsayin wata kasa mara tausayi da jin kai domin yadda take tsare da wani Ba'amarike.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yace akwai rashin tausayi kan yadda kasar Cuba take ci gaba da tsare wani ba Amurka mai suna Alan Gross ba bisa ka’ida ba.

Jiya Talata John Kerry ya gayawa wakilan majalisar dattijai cewa Amurka tana daukan matakai daban daban na neman ganin an sako Gross, wanda aka kama tun a shekarar 2009, wanda aka caja da laifin sayar da na’urorin sadarwa a cikin kasar ba bisa ka’ida ba. Aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 15.

Tunda farko a jiya talatan zaman bada shaida gaban wani kwamitin majalisar dattijai, shugaban hukumar raya kasashe masu tasowa ta Amurka USAID Rajiv Shah yace alhakin ci gaba da tsare Gross yana kan hukumomin Cuba.

Batun nasa ya kara sarkakiya saboda rahoton da kamfanin dillancin labarai na AP ya wallafa makon jiya cewa hukumar USAID ta dauki nauyin kafa wata kafar sadarwa a Cuba tsakaninkanin 2010-2012.

Rahoton na AP yace burin kafa hanyar sadarwa shigen Twitter a Cuba, shine domin ya ingiza mutane su tada kayar bayan, yiwa gwamnatin Cuba mai bin akidar kominisanci zagon kasa.

Shi dai Alan Gross, yana yiwa hukumar USAID aiki ne a matsayin dan kwangila lokacinda hukumomin Cuba suka kama shi.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG