Jumma’a, Fabrairu 12, 2016 Karfe 19:06

  Labarai / Sauran Duniya

  Sakatariya Hillary Clinton zata gana da shugabannin Isra'i'la da Falasdinu

  Yau litinin ake sa ran sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton zata gana da jami’an Isra’ila da na yankin Falasdinu.

  Sakatariya Amurka Hillary Clinton
  Sakatariya Amurka Hillary Clinton

  Yau litinin ake sa  ran sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton zata gana da jami’an Isra’ila da na yankin Falasdinu. Shawarwarin da  zasu yi maida hankali ne kan shirin zaman lafiya tsakanin su, ci gaba da aka samu a Masar, al’amura  a Syria da kuma Iran.

  Sakatariya Clinton ta gana da shugaban yankin Falasdinu Mahmoud Abbas a fara rangadin kusan makonni biyu da zata yi a yankin.Tana son ta tattauna da shugabannin Isra’ila kan wasikun da sassan biyu suka yi musaya a baya bayan nan, yayinda ake ci gaba da shirin wanzar  da zaman lafiya ba tare da sassan biyu sun zauna teburi daya ba.

  Sakatariya Clinton tayi tattaki zuwa birnin kudus daga Masar, inda ta tattauna batun tallafin ta fuskar tattalin arziki da shugaba Morsi da  Field Marshall Mohammed Hussein Tantawi. Wakilin Muryar Amurka Scott Stearns wanda yake cikin ‘yan jarida dake tafiya da  sakatariya Clinton, yace dukkan shawarwari da zata yi a Isra’ila zasu tabo batun rawar da Masar zata taka wajen ganin an tabbatar  da zaman lafiya a yankin, da kuma tabbacin da Mr. Morsi ya baiwa sakatariya Clinton cewa Masar zata mutunta yarjejeniyar  zaman lafiya da  Masar ta kulla da Isra’ila a 1979.

  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye