Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sama da Mutane Dubu Goma Ne Suka Arce Daga Gidajen Su


'yan Gudun Hijira
'yan Gudun Hijira

Dangane da rikicn da yaki ci yaki cinyewa a wasu jahohi biyu dake kasar Sudan, jama'a da dama ne rikicin ya tilastawa barin muhallan su.

Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya yayi Allah wadai da fadan da akeyi a jihohi biyu na arewacin Sudan ta Kudu, da kuma watsi da yarjejeniyar tsagaita wuta wadda gwamnati da ‘yan tawaye suka rattaba wa hannu tun farkon shekarar data wuce.

A wata sanarwar da ya gabatar a daren jiya Lahadi, kwamitin yace rashin bin dokar da sojojin gwamnatin suka yi ya tilastawa mutane sama da dubu 100 arcewa daga gidajen su, harda kuma kawo cikas ga masu aikin jin kai a yankin.

Kwamitin ya kuma dorawa ‘yan tawayen alhakin harin da suka kai garin Malakal dake jihar Nile.

Kungiyar kasashen gabashin Afirka na kokarin shiga tsakanin rikicin da ake tsakanin gwamnatin shugaban Salva Kiir da ‘yan tawayen dake goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar, tana mai cewa tana matukar bakin ciki kan tashin hankalin da ‘yan tawayen suka yi a Malakal.

Kungiyar ta bunkasar tattalin arzikin kasashen gabashin Afirka da ake cewa IAD a takaice, tayi kira ga ‘bangarorin biyu da su mutunta ka’idodin yarjejeniyar da suka kulla don samun hanyar lumana da zata kawo karshen tashin hankalin.

XS
SM
MD
LG